Bangaren kasa da kasa, kasar na ci gaba da fuskantar matsaloli na siyasa da rashin kwanciyar hankali tun bayan da shugaban kasa dan kungiyar yan uwa musulmi ya karbi shugabancin kasar, wanda ake bayyana shi da cewa ba zai iya yin mulki kasa kamar masar ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, gwamnati da jami'an tsaron kasar Masar sun tabbatar da labarin kashe mutum guda daga cikin masu zanga-zangar kasar bayan sakamakon wani rikici da ya barke tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar nuna rashin amincewa da yadda gwamnatin Muhammad Morsi take gudanar da lamurranta a lardin Dakahliya na kasar.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya jiyo wani jami'in tsaron kasar ta Masar yana cewa mutum guda ya mutu kana wasu talatin daga cikin masu zanga-zangar da kuma wasu 10 daga cikin 'yan sandan sun sami raunuka biyo bayan wannan taho mu gamar da ya faru a lokacin da masu zanga-zangar suka taru a gaban ofishin karamar hukumar lardin.
Har ila yau wasu rahotannin kuma sun ce wasu masu adawa da gwamnatin Morsin sun kai hari wani ofishin 'yan sanda dake garin bakin ruwa na Port Said inda a nan ma dai ana sami wasu da suka sami raunuka cikinsu kuwa har da jami'an tsaron.
Cikin 'yan watannin nan dai masu adawa da gwamnati shugaba Morsi na kungiyar Ikhwan Muslimin sun matsa kaimi wajen ci gaba da fitowa zanga-zanga don nuna rashin amincewarsu da yadda yake gudanar da mulkin kasar suna masu zarginsa da mika wuya ga bukatun kasashen yammaci.
1198477