Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar wadda kungiyar ikhwanul muslmin ke jagoranta na cikin wani mawuyacin hali sakamakon abubuwan da suke ta faruwa a kasar na tashin hankali da rashin tsaro a wasu manyan biranan kasar sakamakon abin da ya biyo bayan rikicn da kasar ta fuskanta bayan sanar da sabon kundin tsarin mulki.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, jami’an sojojin kasar Masar sun musanta cewa an basu umurnin karban aikin kula da harkokin tsaron birnin Port Saedd na arewa masu gabacin kasar inda ake fama da tashe tashen hankula.
Kamfanin dillancin labaran kasar masar ya nakalto Mohammad Mohammad Ali kakakin sojojin kasar ta Masar yana cewa aikin sojojin kasar a birnin Port Saeed ya takaida ga kare ma’aikatun gwamnati da kuma wurare masu muhimmanci a cikin birnin, Mohammad Ali ya kara da cewa jami’an tsaro karkashin ma’aikatar cikin gida har yanzun su ne da nauyin tabbatar da harkokin tsaro a birnin.
Kakakin ya musanta labaran da aka yada na cewa shugaba Muhammad Mursu ya bawa sojojin kasar Umurnin karban kula da harkokin tsaro a birnin na Port Saeed . Har’ila yau ofishin shugaban kasa ma ta musanta wannan labarin ta kuma bayyana cewa har yanzun sojojin kasar masar suna nan kan matsayinsu na kula da harkokin tsaron kasa ne, amma ban a cikin gida ba.
1200058