Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, shugaban kasar Senegal maki sal ya bukaci da a gudanar da gyara amakarntun addini musamman ma na kur’ani da suke cikin Senegal domin kauce sake afkuwar irin hadarin da ya faru a cikin wannan mako a wata makarata wanda yay i sanadiyyar mutuwar mutane da dama daga cikin daliban wannan mkaranta.
A wani labarin kuma rahotanni daga kasar Senegal sun habarta cewa sojojin kasar uku tare da wani dan kasar Faransa guda sun rasa rayukansu a wata taho mu gama da suka yi da wasu amsu dauke da makamai a yankin Kazamans da ke kudancin kasar.
Rahotannin sun ce an yi dauki ba dadin ne tsakanin sojojin gwamnatin Senegal da kuma wasu 'yan bindiga da ake zaton cewa mayakan 'yan aware na kudancin kasar kasar ne, wadanda suke fafutuka domin ballewa daga kasar Senegal tare da kafa kasarsu ami cin gishin kanta a yankin Kazamans, wanada akasarin mazauna yankin mabiya addinin kirista ne.
Wata majiyar gwamnatin Senegal ta bayyana cewa, babu tabbataci kan cewa ko mutumin dan kasar Faransa ya mutu ne sakamakon musayar wutar da aka yi tsakanin sojojin gwamnatin da 'yan awaren, amma dai wadanda abin ya shafa suna ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
1200047