Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta yi kira kan muhimmancin samar da zaman lafiya mai dorewa akasar Bangaladash tare da kawo karshen rikicin da kasar take fama da shi a cikin yan lokutannan wanda ya yi sanadiyar mutuar mutane da dama.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na OCI cewa, kungiyar kasashen musulmi ta yi kira kan muhimmancin samar da zaman lafiya mai dorewa akasar Bangaladash tare da kawo karshen rikicin da kasar take fama da shi a cikin yan lokutannan wanda ya yi sanadiyar mutuar mutane da dama sakamakon yanke hukuncin kisa kan wani mai adawa da gwamnati da aka y akasar.
Wasu rahotannin sun ce yan sanda a kasar Bangaladash sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye kan masu goyon bayan shugabar yan adawa na kasar, wadanda suke kokarin hana jami'an tsaron fitar da ita daga gidan da take zaune a cikinsa fiye da shekaru 40.Gidan telbijin na kasar ya bayyana cewa mutane kimani 50 suka ji rauni, a lokacin da yansanda suka yi harbi da harsasan roba da kuma hayaki mai sa hawaye.
Tsohuwar Piraministan kasar ta Bangaladesh Begun Khalida Zia, tana zaune a gidan ne tun lokacin da aka kashe mijinta, tsohon shugaban kasar Janar Ziyau rrahma a wani juyin mulkin da aka yi masa.Sannan gwamnati ta bada gidan ga Khalida Zia a shekara ta 1982. Amma gwamnatin Priminista mai ci Sheikh Hasina ta kwace gidan da nufin tsugunar da iyalan sojojin da suka rasa rayukansu wajen bautawa kasar.
1200010