Kamdfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dilalncin labaran sana cewa, babban majalisar malaman kasar Syria ta bayar da fatawar halasta shiga cikin yakin kasar domin taimaka ma sojojin kasar wajen yaki da 'yan ta'ada da kasashen yammacin turai gami da munafukan larabawa suke daukar nauyinsu da taimaka musu da makamai gami dab a su horon soji a cikin wasu kasashen makwafta.
Jaridar Der Spiegel ta kasar Jamus ta bayar da rahoton da ke cewa Amurkawa suna horar da masu tayar da kayar baya na kasar Syria a cikin wasu sansanonin sojin kasar Jordan.
Jaridar ta bayar da rahoton ne a bugunta na jiya Lahadi, inda ta ce ta samu bayanan daga wasu daga cikin wadanda suka samu wannan horo a kasar Jordan, wadanda suka tabbatar mata da cewa Amurkawa ne suka horar da su, kuma za su shiga cikin kasar Syria domin ci gaba da kai hare-hare, domin hambarar da gwamnatin shugaba Assad.
A nata bangaren jaridar The Guardian ta kasar Birtaniya, ta bayar da wani rahoto makamancin wannan, wanda ke cewa sojojin Birtaniya da na Faransa suna taimaka sojojin na Amurka wajen horar da masu tayar da kayar baya a kasar a cikin sansanonin sojin kasar Jordan.
Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Amurka ta Pentagon yaki ya ce uffan a lokacin da aka tambaye gaskiyar wannan labari, kamar su ma'akatun harkokin waje da na tsaro na kasashen Faransa da Birtaniya suka ki cewa komai kan hakan.
1202474