IQNA

Malaman Addini A Senegal Ba Su Amince Da Rufe Makarantun Kur'ani Ba

16:53 - March 11, 2013
Lambar Labari: 2509822
Bangaren kasa da kasa, manyan malamin addini a kasar Senegal sun nuna rashin amincewarsu da matakan da mahukuntan kasar suke nufin dauka na rufe wasu daga cikin makarantun addini a kasar da sunan rashin cika sharuddan da aka gindaya musu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, malaman addini a kasar Senegal sun nuna rashin amincewarsu da matakan da mahukuntan kasar suke nufin dauka na rufe wasu daga cikin makarantun addini a kasar da sunan rashin cika sharuddan da aka gindaya musu wanda suka ce bas u san da haka sai yanzu da matasal ta faru.

A wani labarin kuma Majalisar dokokin Kungiyar Raya Harkar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirika ta ECOWAS ta bukaci kasashen da suke mambobi ne a kungiyar da su dauki matakin aiwatar da dokar kame jagororin kungiyoyin 'yan tawayen Mali.
A karshen zaman taron gaggawa irinsa na farko da Majalisar Dokokin Kungiyar Raya Harkar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirika ta ECOWAS ta gudanar a wannan shekara ta 2013 a cibiyarta da ke birnin Abuja fadar mulkin tarayyar Nigeriya a jiya Alhamis ta amince da dokar cafke jagororin kungiyoyin 'yan tawayen Mali, don haka shugaban Majalisar Dokokin Kungiyar Ike Ekweremadu ya bayyana cewar aiwatar da wannan doka zata zame darasi ga sauran kungiyoyin 'yan ta'adda.
Kungiyar Raya Harkar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirika ta ECOWAS a halin yanzu haka tana da mambobi goma sha biyar ne da suka hada da Benin, Burkina Faso, Cape Verde, Gambiya, Ghana, Jamhuriyar Guinea, Guinea Bissau, Ivory Coast, Liberiya, Mali, Jamhuriyar Niger, Nigeriya, Senegal, Saliyo da Togo.
1202280




captcha