IQNA

Kungiyar kasashen musulmi ta yi fatan yin aiki tare da fadar Vatican

16:51 - March 15, 2013
Lambar Labari: 2511395
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen kasashen musulmi ta yi fatar yin aiki tare da fadar Vatican musamman bayan zaben da aka yi wa sabonpaparoma da ake fatan zai mayar da hankali wajen kara karfafa fahimtar juna tsakanin mabiya addinin kirista da kuma musulmi.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, kungiyar kasashen kasashen musulmi ta yi fatar yin aiki tare da fadar Vatican musamman bayan zaben da aka yi wa sabonpaparoma da ake fatan zai mayar da hankali wajen kara karfafa fahimtar juna tsakanin mabiya addinin kirista da kuma musulmi na duniya baki daya.

A ranar Laraba da ta gabata ce Cardinals Cadinal na dirikar Roman Catholic a birnin Vatican suka zabi Cardinal Jorge Bergoglio a matsayin Paparoma na darikar, wanda kuma ya bawa kansa suna Francis. Sabon Paparoman dai dan asalin kasar Argentina shi ne paparoma na farko a wajen nahiyar Turai, har ila yau shi ne Paparoma na farko daga yankin Amurka na lokaci mai tsawo. Dan shekara 76 Paparoma Farncis ya bawa kansa wannan sunan ne watakila don fatan yin koyi da salon rayuwan Paparoma St Francis Assisi wanda ya rayu a cikin karni na 13 miladiyya, wanda kuma ya nuna zuhudu a matsayin tafarkin sauya yadda ake tafiyar da chuchin, duk da cewa daga bayan ya fi karkata ga abinda duniya fiye da yadda ya soma.

Paparoma Benedik wanda ya gada ya fi shi da shekaru biyu ne kacal a lokacinda shima ya zama paparoma a shekara ta 2005, don haka ne Cardinal Karl Lehman na kasar Jamus yake cewa mai yuwa shima ya yi murabus kamar yadda wanda ya gada ya yi. Duka da cewa wadanda suka san shi sun ce yana da koshin lafiya , sai dai tarihin rauwarsa ya tabbatar da cewa Paparoma Bergoglio dai ya taba samun matsa huhu, wanda ya sa aka cire masa bangare guda na huhunsa. Paparoma Francis dais hi ne paparoma na 266 a jerin shuwgabannin cocin da aka yi ya zuwa yanzu.

1204506






















captcha