Bangaren siyasa, wanda ya jagoranci sallar Jma'a a yau a nan birnin Tehran ya bayyana cewa, takunkumin da kasashen yammacin turai suka kakabawa Iran ba zai iya hana kasar ci gaban da take samu ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto aga bangaren yada labaransa a birnin Tehran cewa , wanda ya jagoranci sallar Jma'a a yau a nan birnin Tehran ya bayyana cewa, takunkumin da kasashen yammacin turai suka kakabawa Iran ba zai iya hana kasar ci gaban da take samu ba.
Sheikh Kazim Saddiqi ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar hudubar sallar Juma'a anan birnin Tehran a yau, inda y ace ko shakkak babu abbabn abin da yake tayawa kasashen yammacin turai hankali shi ne, yadda suka kakaba mata takunkumin day a kama a ce kasar ta durkushe baki daya, amma kuma kuma akullum rana kasar na kasar samun ci gaba adukkanin bangarori.
Dangane da zabukan da za agudanar a kasar kuwa nan 'yan lokuta nan da kimanin watanni biyu masu zuwa, malamin ya jaddda cewa al'ummar kasar za sub a maras da kunya, domin kuwa za su fito kwansu da kwarkatarsu domin bata wa makiya yaji a ido ta hanyar kada kuri'arsu.