IQNA

Ayatollah Kermani Ya Jadda Cewa Gudanar Da Zabe Wajibi Ne Na Addini

23:52 - April 12, 2013
Lambar Labari: 2518034
Bangaren siyasa, wanda ya jagoranci sallar Juma’a abirnin Tehran Ayatollah Kermani ya jadda cewa fitowar jama’ domin kada kuri’unsu wajibi na addini da ya kamata su safke domin hakan shi ne abin da ke tabbatar da hakkin kowa wajen zaben shugaba kuma hakan shi ne abin da ke tabbar wa duniya sabanin farfagandar da ake yi kan jamhuriyar muslunci.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa abirnin Tehran, cewa, wanda ya jagoranci sallar Juma’a abirnin Tehran Ayatollah Kermani ya jadda cewa fitowar jama’ domin kada kuri’unsu wajibi na addini da ya kamata su safke domin hakan shi ne abin da ke tabbatar da hakkin kowa wajen zaben shugaba kuma hakan shi ne abin da ke tabbar wa duniya sabanin farfagandar da ake yi maras tushe.
Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran ya jaddada cewar al’ummar Iran zasu sake daukan matakin kunyata makiya a yayin gudanar da zaben shugaban kasa a Iran a cikin watan Yunin wannan shekara.
A hudubar sallar Juma’arsa ta yau Ayatullahi Muhammad Ali Muwahhidi Kirmoni ya jaddada cewar da yardan Allah al’ummar Iran zasu sake fitowa kwansu da kwarkwatarsu a yayin zaben shugaban kasa a cikin watan Yunin wannan shekara ta 2013, tare da jaddada goyon bayansu ga tsarin Musulunci a kasar Iran, lamarin da zai kara rusa makirce-makircen da makiya ke kitsawa kan kasar Iran da sanya makiyan ga fitar da rai kan kasar Iran.
Ayatullahi Kimoni ya kara da cewa: Zaben shugaban kasa na bana a Jamhuriyar Musulunci ta Iran zai zo ne a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da fuskantar matsin lamba tare da takunkumi da kuma bakar farafagandar siyasa daga bangarori daban daban na makiya, amma shakka babu al’ummar Iran zasu mai da gagarumin martani ga makiyansu a lokacin zaben.
Har ila yau Ayatullahi Muhammad Ali Kirmoni ya mika ta’aziyya ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu ko suka jikkata sakamakon girgizar kasa da aka yi a lardin Bushahar da ke kudancin kasar Iran tare da jinjinawa kungiyoyin bada agaji ta Iran kan gagarumin rawar da suka taka wajen tallafawa al’ummar yankunan da girgizar kasa ta ritsa da su.

1211632
captcha