IQNA

Gasar Kur’ani mai Tsarki Ta Jami’ar Azhar Da Ke Kasar Masar

23:50 - April 12, 2013
Lambar Labari: 2518036
Bangaren kasa da kasa, babbar gasar karatun kur’ani mai tsarki ta jami’ar Azhar da ke birnin Alkahira na kasar masar tana gudana adaidai lokacin da kasar take fuskantar matsalolin siyasa musamman tsakannin kungiyar ikhwan masu mulki da kuma ‘yan adawa wadanda bas u amince da manufofin kungiyar ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, yanzu haka babbar gasar karatun kur’ani mai tsarki ta jami’ar Azhar da ke birnin Alkahira na kasar masar tana gudana adaidai lokacin da kasar take fuskantar matsalolin siyasa musamman tsakannin kungiyar ikhwan masu mulki da kuma ‘yan adawa wadanda bas u amince da manufofin kungiyar ba wadanda ake zargin ana son saka su cikin harkokin mulki.
A wani labarin kuma Kakakin shugaban kasar Masar ya karyata labarin da ke cewa an shayar da shugaban kasar Masar Muhammad Morsi guba, a taron manema labaran da ya gudanar a yau Alhamis: Kakakin shugaban kasar Masar Iyhab Fahami ya bayyana jita-jitar da ke yawo a wasu shafukan sadarwar yanar gizo-gizo wato Internet da ke da’awar cewa: An shayar da shugaban kasar Masar Muhammad Morsi guba da cewa maganganu ne marassa inganci da tushe kuma karya ce tsagwaronta.
Tun a jiya Laraba ce wasu bayanai a shafukan sadarwar Internet daga kasar Masar suke yada batun shayar da shugaba Muhammad Morsi guba tare da bayyana cewar shugaban yana cikin mummunan hali, har ila yau kakakin shugaban kasar ta Masar Iyhab Fahami ya musanta batun yiyuwar gudanar da garambawul a gwamnatin fira ministan Hisham Qandil a cikin ‘yan kwanakin nan kamar yadda wasu kafafen watsa labaru ke bayyanawa.
1211563




captcha