IQNA

Dole Ne Shugaban Kasa Da Za A Zaba Ya Zama Mai Tunani Kan Rayuwar Talakawa

20:26 - April 27, 2013
Lambar Labari: 2524787
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubun dubatan ma'aikatan kasar Iran, ciki kuwa har da wasu ma'aikatan da suka nuna gwaninta a bangarori daban-daban na kasar ta Iran don tunawa da ranar ma'aikata ta kasa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a safiyar yau asabar ce jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubun dubatan ma'aikatan kasar Iran, ciki kuwa har da wasu ma'aikatan da suka nuna gwaninta a bangarori daban-daban na kasar ta Iran don tunawa da ranar ma'aikata ta kasa wadda aka saba gudanrwa a kowace shekara.
A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen wannan ganawar, Jagoran ya yi ishara da irin bukatar da kasar Iran take da ita wajen gudanar da wani gagarumin yunkuri a fagen tattalin arziki da siyasa inda ya bayyana fitowa a lokacin zaben shugaban kasar da za a gudanar a matsayin wani lamari mai muhimmanci a fagen nuna irin karfi na kasa da ake da shi, kamar yadda kuma ya kirayi 'yan takaran shugaban kasar a zaben da za a gudanar nan gaba da su dubi sosai cikin irin karfi da kuma kwarewar da suke da ita saboda muhimmancin da matsayin shugaban kasa yake da shi cikin tsarin gudanar da kasa. Jagoran ya ci gaba da cewa: Kasa da kuma al'ummar Iran masu girma da gwagwarmaya suna bukatar wani shugaban kasa mara tsoro sannan jarumi a fagen kasa da kasa da kuma fada da ma'abota girman kai, sannan a fagen cikin gida kuma ma'abocin hikima, tsare-tsare masu kyau, wanda ya yi imani da tsarin tattalin arziki mai tinkarar makiya, ma'abota tsarkin zuciya, mai nesantar abubuwa masu haifar da rikici sannan muka ma'abocin take na hakika da ya yi daidai da hankali.
Yayin da yake magana kan ma'aikata da kuma siffofin da suke da su, Ayatullah Khamenei ya bayyana ma'aikatan a matsayin wani tushe na ci gaba da kuma zaman lafiyan kasa inda ya ce: Ma'aikata su ne tushen al'umma, ta yadda idan aka rasa su ko kuma suka yi rauni, to kasa za ta gurguce.
Har ila yau Jagoran ya jaddada wajibcin ba wa batun aiki da ma'aikata muhimmanci a fagen gina kasa da kuma kafa dokoki na gudanarwa yana mai cewa: Matukar ma'aikata suka samu kwanciyar hankali, jin dadi da lamuni na aiki, to za a sami ci gaba cikin sauki sannan kuma cikin gaggawa.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin rawar da ma'aikata suka taka wajen nasarar da juyin juya halin Musulunci ya samu a kasar Iran da kuma lokuta daban-daban bayan hakan ciki kuwa har da lokacin kallafaffen yaki, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa ya yi: Tsawon shekaru 34 da suka gabata, an yi kokari daban-daban wajen sanya ma'aikata su yi fito na fito da juyin juya halin Musulunci da tsarin Musulunci na Iran, to amma ma'aikatan na Iran sun tsaya kyam wajen tinkarar wannan makircin. Lalle hakan abin alfahari ne ga ma'aikatan.
Har ila yau kuma yayin da ya ke ishara da sanya wa shekarar da ta gabata sunan 'Shekarar Goyon Bayan Kayayyakin Cikin Gida Da Jari Na Dan Kasa', Jagoran ya ce goyon bayan kayayyakin da ake samarwa a cikin kasa ba wani lamari ne da ya takaita kawai ga shekara guda ba. Wajibi ne a ci gaba da hakan da kuma ba shi muhimmanci. Kamar yadda kuma yayi ishara da muhimmanci da kuma wajibcin da ke cikin amfani da kayayyakin da ake yi a cikin gida.
A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da umurnin Musulunci da karfafa aiki da kuma girmama ma'aikata bugu da kari kan samar musu da lamuni na aiki inda ya ce: Sabanin tsarin gurguzu da jari hujja, addinin Musulunci ya dau matsaya ta tsaka-tsaki ne, ta yadda yake kallon ma'aikata da mahanga ta dan'adamtaka da kuma adalci.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Irin zanga-zangogin da a yau ake ganin suna faruwa a Turai da Amurka, babban dalili ne da ke nuni da rashin ingancin tsarin jari hujja.
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Abin da ke faruwa a Amurka da Turai, mafarin aiki ne, yanayin zai ci gaba da muni. Don kuwa tsarin jari hujja ya kama hanyar faduwa kasa warwas. Jagoran ya ci gaba da cewa: Matsalolin tattalin arzikin da ke faruwa a halin yanzu a kasashen yammaci, wani bangare ne na rashin ingancin ci gaban yammaci, wanda matsaloli na kyawawan halaye da al'adu ma wani bangare ne na irin wadannan matsalolin.
Har ila yau kuma yayin da yake magana kan sanya wa shekarar bara sunan shekarar "Kumaji na tattalin arziki da siyasa' Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar wajibi dukkanin tsare-tsaren da za a gudanar su zamanto wajen kyautata rayuwar raunanan mutanen cikin al'umma.
Yayin da koma kan zaben shugaban kasar da za a gudanar nan gaba, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi al'ummar kasar da su ba da himma wajen fitowa kwansu da kwarkwatarsu a lokacin zaben.
Ayatullah Khamenei ya ce: har ya zuwa yanzu bayan shekara da shekaru na makirce-makirce da ma'abota girman kai suke yi wa al'ummar Iran amma har yanzu ba su fahimci irin tsayin dakan al'ummar Iran din ba, kuma a nan gaba ma haka lamarin zai kasance.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana zabe a matsayin mafi muhimmancin fagen bayyanar karfi irin na al'umma inda ya ce: Al'ummar da ta kasance a raye sannan kuma ta dogara da irada da karfi na Ubangiji, to kuwa za ta yi nasara a dukkanin fagage ciki kuwa har da fagen zabe.
Jagoran juyin juya halin Musulunci har ila yau yayi karin bayani kan siffofin da ya kamata 'yan takaran shugabancin kasar su kasance suna tare da su ciki kuwa har da hikima, daukaka ta kasa, aiki tukuru da sauransu yana mai fatan cewa al'ummar Iran za su fitowa kwansu da kwarkwatansu a lokacin zaben.

1218685


captcha