IQNA

Yusuf Qardawi ya sake yin Dirar mikiya kan mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah

20:26 - April 27, 2013
Lambar Labari: 2524788
Bangaren kasa da kasa, malamin gwamnatin kasar Qatar Yusuf Qardawi wanda ya shahara da tsananin kiyayya ga mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah ya sake yin dirar mikiya kan mabiya mazhabar shi'a musamman Iran da kuma kungiyar Hizbullah da fira ministan kasar Iraki Nuiu Maliki.
Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, Yusuf Qardawi wanda ya shahara da tsananin kiyayya ga mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah ya sake yin dirar mikiya kan mabiya mazhabar shi'a musamman Iran da kuma kungiyar Hizbullah da fira ministan kasar Iraki Nuiu Maliki tare da yin kira ga 'yan sunna das u gaba da kaddamar da hare-haren ta'addanc a cikin Iraki da sunan kare kai.
A nasa bangaren fira ministan Iraki Nuri Al-Maliki ya yi gargadi kan makirce-makircen da wasu ke kitsawa da nufin ganin sun wurga kasar Iraki cikin yakin basasa, a jawabin da ya gabatar ta gidan talabijin din gwamnatin Iraki a yau Alhamis: Fira ministan kasar Iraki Nuri Al-Maliki ya bayyana cewar wasu gungun jama'a masu dauke da makamai suna kokarin ganin sun kunna wutar yakin basasa ta hanyar rikicin mazhaba a kasar Iraki lamarin da zai shafi kowa da kowa, domin fitina ba ta rabe tsakanin mutumin kirki da mutumin banza.
Nuri Al-Maliki ya jaddada cewar kasar Iraki kasa ce take bukatar zaman lafiya da samun fahimtar juna tsakanin dukkanin al'ummar kasar domin samun damar gina sabuwar Iraki da al'ummarta zasu rayu cikin aminci da tsaro, Al-Maliki ya yi kakkausar suka kan mummunar rawar da wasu kasashen yankin gabas ta tsakiya ke takawa na ganin sun wargaza kasar Iraki domin cimma wasu munanan manufofinsu.
Mahukuntan Iraki dai sun sha fitowa fili suna zargin kasashen Saudiyya, Qatar da Turkiyya da hannu a kunna wutar rikici a Iraki ta hanyar tallafawa kungiyoyi 'yan ta'adda da suke da'awar addini da nufin tarwatsa kasar.
1218771



captcha