IQNA

Sayyid Nasrullah Ya Gargadi Makiya Kan makircin Da Suke Kullawa A Kan Syria

13:46 - May 01, 2013
Lambar Labari: 2527084
Bangaren kasa da kasa, a wani jawabi da ya gabatar jiya Talata wanda gidan talabijin Almanar mallakin kungiyar Hizbullah tare da wasu kafofin yada labarai suka watsa kai tsaye ya gargadi makiya al'ummar musulmi da su shiga taitayinsu kan yunkurinsu na haifar da rikici a cikin mazhaba akasar Syria da nufin rusa kasar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana cewar ya kamata kasashen yammaci su fahimci cewa kasar Siriya tana da kawaye na hakika wadanda ba za ta taba bari a kifar da gwamnatinta kasar ba.
Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne cikin wani jawabi da ya yi a daren jiya wadda tashar talabijin din Al-Manar mallakar kungiyar Hizbullah din ta watsa kai tsaye inda yayin da yake magana kan rikicin da ke gudana a kasar Siriya da kuma dalilan ci gaba da wannan rikicin ya bayyana cewar: manufar wannan rikicin ita ce ruguza kasar Siriyan dan biyan bukatun yahudawan sahyoniya.
Yayin da ya ke magana kan gazawar da masu adawa da kasar Siriyan suka yi wajen kifar da gwamnatin kasar, Sayyid Nasrallah ya ce hanya guda kawai ta magance matsalar kasar Siriyan ita ce hanyar tattaunawa tsakanin bangarori daban-daban na al'ummar kasar yana mai jan kunnen kasashen da suke son kifar da gwamnatin Siriyan da cewa kawayen Siriyan ba za su barsu su cimma wannan bakar aniyar da suke da ita ba.
Har ila yau kuma Sayyid Nasrallah ya yi kakkausar suka ga wasu malaman da suke fitar da fatawoyin da suke halalta jinin al'ummar Siriya, kamar yadda kuma ya ja kunnen 'yan ta'addan kasar da gwamnatocin da suke goya musu baya wadanda suke shiri kai hari haramin Sayyida Zainab (a.s) da ke birnin Damaskus da cewa kungiyar da sauran al'umma ba za su taba barinsu su cimma wannan bakar aniyar ta su ba.

1220980

captcha