IQNA

Jagoran juyin juya hali Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da jami'ai da ma'aikata

21:40 - May 15, 2013
Lambar Labari: 2534274
Bangaren siyasa, a safiyar yau Litinin ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da jami'ai da ma'aikata masu gudanar da ayyukansu a fagen fasahar gwagwarmaya da adabin juyin juya halin Musulunci na kasar Iran.
A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen wannan ganawar, Jagoran ya bayyana samar da gagarumin yunkuri mai karfafa gwiwa a fagen adabi na gwagwarmaya da juyin juya halin Musulunci haka nan kuma da kawo karshen kokarin da wasu masu adawa da juyin juya halin Musuluncin suke yi wajen mayar da shi saniyar ware da kuma boye ma'anoni da kuma hakikanin juyin a matsayin wasu siffofi guda biyu masu muhimmanci a wannan fage na adabi inda ya ce: Wannan yunkuri mai tasirin gaske ya sanya kasar Iran ta zamanto ba ta bukatar adabin da aka shigo da shi daga waje.
Har ila yau yayin da ya ke ishara da kokarin da wasu da suke kiran kansu da sunan masana suke yi wajen boye hakikanin gagarumin yunkurin wannan juyi na Musulunci da kuma lamurran da suka shafe shi, Jagoran ya bayyana cewar: karin haske kan irin gagarumar dama ta sanin Ubangiji da wannan juyi na Musulunci ya samar daga bakin masana adabi masu riko da koyarwar juyin lamari ne da zai sauya irin tunani na kuskure dake cikin rubuce-rubucen irin wadancan masanan da suka dogara da tarjama sannan kuma ya share fagen samar da abubuwan alfahari a fagage daban-daban na adabi.
Haka nan kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi kira da a ba wa batun fadada bincike cikin ayyuka na adabi da fasaha muhimmanci, sai dai kuma ya ja kunnen dangane da dogaro da hanyoyin ‘yan kasashen yammaci kawai a wannan fagen yana mai kiran da a yi kokari wajen kirkiro wasu abubuwa da suka dace da koyarwa da kuma al'adu na cikin gida.
Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana wajibcin dubi a aikace cikin kallafaffen yaki na shekaru takwas da aka kallafa wa Iran da kuma sauran yakukuwan da suka faru a wannan zamanin da kuma kwatanta juyin juya halin Musulunci na Iran da sauran juyin juya halin da suka faru a kasashen duniya yana mai cewa: Akwai gagarumin bambanci tsakanin juyin juya halin Musulunci na Iran da sauran juyin juya halin da suka faru a duniya a bangaren karfi da kuma abubuwan da suka samar. To sai dai kuma sabanin sauran juyin juya halin na duniya, ba a ba wa juyin juya halin Musulunci na kasar Iran hakkinsa a bangaren adadi da rubuce-rubuce.
Kafin jawabin Jagoran dai sai da wasu daga cikin mahalarta taron suka gabatar da jawabinsu da kuma bayyanar da mahangarsu dangane da batutuwan da ake magana a kai.


1228850






captcha