IQNA

Yahudawan Sahyuniya Na Da Shirin Rarraba Birnin Qods Mai Alfarma

21:40 - May 15, 2013
Lambar Labari: 2534275
Bangaren kasa da kasa, haramtacciyar kasar Isra'ila na shirin rarraba dukkanin yankunan birnin Qods da nufin mayar da birnin fadar mulkinta kamar yadda ta shirya tun shekaru fiye da hamsin da suka gabata tare da mayar da sauran palastinawan yankin yan gudun hijira.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanr gizo na kwamitin zartarwa na kungiyar Hamas cewa haramtacciyar kasar Isra'ila na shirin rarraba dukkanin yankunan birnin Qods da nufin mayar da birnin fadar mulkinta kamar yadda ta shirya tun shekaru fiye da hamsin da suka gabata tare da mayar da sauran palastinawan yankin yan gudun hijira kamar yadda suka yi saka yi da sauran palastinawa da ke wasu yankuna.

A yau ne al’ummar Palasdinawa su ke tunawa da ranar da aka kirkiro Isra’ila akan gurbin kasarsu. A garin Ramallah, cibiyar gwamnatin kwarya-kwarya ta Palasdinu, dubun dubatar Palasdinawa sun taru dauke da tutocin kasarsu da makullan gidajensu da ‘yan sahayoniya su ka kwace.

Da ya ke gabatar da jawabi dangane da wannan ranar, shugaban palasdinawa Mahmud Abbas Abu Mazin ya ce; “Duk da kokarin da aka yi na rabamu da al’adunmu da tarihinmu, mun yi nasarar akan hakan.” Mahmud Abbas ya kara da cewa; Babu wata kasa a duniyar nan a wannan lokacin daga ciki hadda Amurka wacce ta ke inkarin hakkin da mu ke da shin a kafa gwamnatinmu akan kasarmu da aka mamaye a 1967.

Shugaban na Palasdinawa ya ci gaba da cewa; A wannan lokacin babu wanda zai iya kore samuwarmu.

1228860

captcha