Bangaren kasa da kasa, wasu daga masana a cikin kasashen larabawa sun amanar cewa babbar manufar gwamnatocin kasashen da suke son su kulla alaka dad a haramatacciyar kasar Isra'ila tare da mika mata yankunan palastinawa da sunan zaman lafiya manufar hakan ita ce saryar da hakkokin al'ummar palastine.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Aldastur ta kasar Jordan cewa, wasu daga masana a cikin kasashen larabawa sun amanar cewa babbar manufar gwamnatocin kasashen da suke son su kulla alaka dad a haramatacciyar kasar Isra'ila tare da mika mata yankunan palastinawa da sunan zaman lafiya manufar hakan ita ce saryar da hakkokin al'ummar wannan yanki da suke fusknatr zaluncin yahudawan sahyuniya.
Bayan cika shekaru 65 karkashin zalunci yahudawa a yau ne al’ummar Palasdinawa su ke tunawa da ranar da aka kirkiro h.k. Isra’ila akan gurbin kasarsu. A garin Ramallah, cibiyar gwamnatin kwarya-kwarya ta Palasdinu, dubun dubatar Palasdinawa sun taru dauke da tutocin kasarsu da makullan gidajensu da ‘yan sahayoniya su ka kwace. Da ya ke gabatar da jawabi dangane da wannan ranar, shugaban palasdinawa Mahmud Abbas Abu Mazin ya ce “Duk da kokarin da aka yi na rabamu da al’adunmu da tarihinmu, mun yi nasarar akan hakan.
Shugaba Mahmud Abbas ya kara da cewa; Babu wata kasa a duniyar nan a wannan lokacin daga ciki hadda Amurka wacce ta ke inkarin hakkin da mu ke da shin a kafa gwamnatinmu akan kasarmu da aka mamaye a shekara ta dubu da dari tara da sittin da bakwai, shugaban na Palasdinawa ya ci gaba da cewa; A wannan lokacin babu wanda zai iya kore samuwarmu.
1228710