IQNA

Jaridar Independent Ta Bayar Da Rahoto Kan Cin Zarafin Musulmin Maynamar

9:08 - May 29, 2013
Lambar Labari: 2540447
Bangaren kasa da kasa, jaridar Independent da ake bugawa akasar Birtaniya ta bayar da wani rahoto dangane da yadda ake cin zarafin musulmin kasar Myanmar da kuma yadda hakan yake barin mummunan tasiri a cikin kwakwalen kanan yara.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, jaridar Independent da ake bugawa akasar Birtaniya ta bayar da wani rahoto dangane da yadda ake cin zarafin musulmin kasar Myanmar da kuma yadda hakan yake barin mummunan tasiri a cikin kwakwalen kanan yara na kasar.

Shugaban komitin kare hakkin bil'adama ta kasar Masar ya bukaci wata kungiyar kare hakkin bil'adama wacce ta tattara bayanai kan take hakkin musulmin kasar Myanmar da ta gabatar da shaidun ga kotun kasa da kasa don nazari da kuma gurfanar da masu laifufuffuka a kisan musulmin na Myanmar. Wani shafin yanar Gizo ta kungiyar "Ikhwan" ya nakalto Izzuddeen Alkumi shugaban komitin kare hakkin bi'adama na majalisar dokokin kasar Masar yana kira ga kungiyar kare hakkin bil'adama ta "Human Right Wach" da ta gabatar da shaidun da ta tara kan kisan musulmin miyanmar ga kotun kasa da kasa da ke birnin Hague. Alkumi har'ila yau yayi kira ga komitin tsaro na MDD ta ya gabatar da abinda ya wajaba a kansa na kare hakkin kananan alummu a kasar Myanmar . Mabiya addinin Buza masu rinjaye a kasar dai tare da hadin ka
i da wasu jami'an gwamnatin kasar suna kisan musulmin kasar Myanmar suna kuma kona gidajensu. A halain yanzu dubbban daruruwan musulmin kasar kasar suka yo gudun hijira zuwa wasu kasashe don tsira da ransu.
1235297




captcha