IQNA

Zaben Shugaban kasa A kasar Iran Zai Baiwa Maras da Kunya

0:01 - June 01, 2013
Lambar Labari: 2541310
Bangaren siyasa, limamin da ya jagoranci sallar juma'a a birnin Tehran na kasar Iran ya jaddada cewar fitowar al'ummar Iran a yayin zaben shugaban kasa lamari ne da zai kara rusa makirce-makircen makiya kan juyin juya halin Musulunci da tsarin Jamhuriyar Musulunci a kasar Iran.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a hudubar sallar juma'arsa ta yau a babban masallacin birnin Tehran Ayatullahi Kazim Siddiqi ya tabo batun gudanar da tace 'yan takarar shugaban kasa tare da amincewa da masu mahanga mabambanta da cewar wata babbar nasara ce, kuma gudanar da zabe ita ce hanyar ci gaba da bin tafarkin marigayi Imam Khomeini, kuma hanya ce ta shahidai da suka sadaukar da rayuwarsu domin samar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, don haka ya bayyana fatansa na ganin al'ummar Iran sun dauki matakin fitowa kwansu da kwarkwatarsu a ranar zabe domin kara tabbatar da wata gagarumar nasarar ta daban domin ta hanyar gudanar da zabe ne ake tantance makomar kasa.

Ayatullahi Siddiqi ya kuma tabo batun Siriya da irin gagarumar nasarar da sojojin gwamnatin kasar ke samu a kan 'yan ta'addan kasa da kasa da aka jige a cikin kasar ta Siriya domin rusata, inda ya bayyana cewar wannan wata nasara ce daga Allah musamman idan aka yi la'akari kan irin munanan matakan da manyan kasashen yammacin Turai karkashin jagorancin Amurka suke ci gaba da dauka na kara ruruta wutan rikicin kasar tare da fadada matakin tura makamai ga 'yan ta'adda da nufin kara zubar da jinin al'ummar Siriya.

1236480









captcha