IQNA

Yan takara Sun Yi Muhawara da junansu dagane da shirinsu na Mulki

23:49 - May 31, 2013
Lambar Labari: 2541311
Bangaren siyasa, dukaknin 'yan talarar nemna shugabancin kasa airan sun yi muhawa, yan takarar shugaban kasa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun gudanar da wata gagarumar muhawara a tsakaninsu kan hanyoyin da kowannensu zai bi wajen tunkarar matsalolin da suke addabar kasar Iran tare da kara habaka ci gabanta.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, gidan talabijin din kasar Iran a yau Juma'a ya gudanar da zaman tattaunawa tsakanin 'yan takarar shugabacin kasar su takwas don jin mahangar kowanne daga cikinsu kan hanyoyin da zai bi wajen tunkarar matsaloli da suke addabar kasar Iran tare da fayyace shirinsa na kara habaka ci gaban kasar.

Dukkanin 'yan takarar su takwas sun fayyace mahangarsu kan harkokin tattalin arziki, siyasa da zamantakewa tare da jaddada aniyarasu ta magance matsalolin da suke addabar al'ummar kasar. Kamar yadda 'yan takarar suka amsa muhimman tambayoyin da al'ummar Iran ke gabatarwa dangane da makomar kasarsu ta fuskoki da dama musamman siyasa, tattalin arziki, al'adu da zamantakewa.

Har ila yau zaman muhawarar ya bada dama ga 'yan takarar kan tattauna mahangar kowane daga cikinsu ta hanyar gabatar da suka ko yabo, inda zaman ya kwashe tsawon sa'o'i hudu ana gudanar da shi, kuma sauran kafofin watsa labaran kasar Iran na ciki da waje suka watsa shirin kai tsaye.


1236434





captcha