IQNA

Jiragen Yakin haramtacciyar kasar Isra'ila Sun Yi Shawagi A Sararin Samaniyar Lebanon

23:57 - June 02, 2013
Lambar Labari: 2542540
Bangaren kasa da kasa, jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suna ta shawagi yau a sararin samaniyar kasar Lebanon domin tsokana wanda kuma hakan ya zo a ne adaidai lokacin da kungiyar Hizbullah take fattatakar mayakan alkaida da kuma sauran kungiyoyi masu kafirta musulmi da ake kira yan tawaye a Syria.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto, ya nakalto daga tashar Almanar cewa, a yau jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suna ta shawagi yau a sararin samaniyar kasar Lebanon domin tsokana wanda kuma hakan ya zo a ne adaidai lokacin da kungiyar Hizbullah take fattatakar mayakan alkaida da kuma sauran kungiyoyi masu kafirta musulmi da ake kira yan tawaye a Syria wanda suke samun goyon bayan Amurka da yahudawa.

Rahotanni da suke fitowa daga kasar Labanon sun tabbatar da cewa dakarun kungiyar Hizbullah ta kasar sun sami nasarar hallaka wani adadi mai yawa na ‘yan ta’addan kungiyar Jabnatun Nusra da ‘yan Jaishul Hur da raunana wasu sakamakon gumurzun da ya barke tsakanin bangarorin biyu a lokacin da ‘yan ta’addan suka so shigowa cikin kasar Labanon din daga kasar Siriya da kai hari garin Ba’alabak da ke yankin Biqa’a na kasar.


Rahotannin sun ce su dai wadannan ‘yan ta’addan sun kawo harin ne ta bangarori daban-daban a daren jiya da nufin kai hari garin na Ba’albak da kuma dana wasu na’urorin harba rokoki da za su yi amfani da su wajen kai hari cikin Labanon din, inda dakarun kungiyar Hizbullah din suka far musu lamarin da ya yi sanadiyyar hallaka ‘yan ta’addan da kuma raunana wasu. Har ila yau rahotannin sun ce mutum guda daga cikin dakarun Hizbullah din ya yi shahada kana wasu kuma sun sami raunuka.

A bangare guda kuma na’ibin babban sakataren kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Qasim ya bayyana cewar kungiyar ta su ba za ta taba bari masu kafirta mutane da sauran ‘yan amshin shatan HKI su haifar da rikici a kasar Labanon ba. Sheikh Qasim ya kara da cewa akwai wani shiri da aka shigo da shi fage na bata sunan kungiyar da kuma kawo karshen gwagwarmayar, to sai dai ya zuwa yanzu sun gagara cimma manufofinsu.

Cikin ‘yan watannin nan dai wasu daga cikin kasashen larabawa bisa goyon bayan kasashen yammaci da kuma HKI sun kaddamar da wani shiri na bakanta sunan kungiyar ta Hizbullah a idon al’ummar larabawa da na musulmi ta hanyar amfani da wasu malaman fada. Daga cikin irin malaman da ake amfani da su wajen cimma wannan manufa ta raba kan al’umma har da shehin malamin nan na fadar sarkin Qatar Sheikh Yusuf Qardawi wanda a shekaran jiya yayi kira ga wadanda ya kira ‘yan Ahlussunna da su tafi kasar Siriya da nufin yakar gwamnatin kasar da kuma kungiyar Hizbullah, lamarin da wani adadi mai yawa na malaman musulmi ‘yan sunnan suka yi Allah wadai da shi da bayyana hakan a matsayin kokarin haifar da fitina a tsakanin musulmi.
1237513



captcha