IQNA

Farfagandar Karya Ta Kafafen Watsa Labaran Yammaci Kan Zaben Iran

19:50 - June 06, 2013
Lambar Labari: 2543435
Bangaren kur'ani, Cikin ‘yan kwanakin nan dai musamman bayan sanar da sunayen ‘yan takaran zaben shugaban kasar Iran da za a gudanar a wata mai kamawa kafafen watsa labaran kasashen yammaci sun matsa kaimi wajen yada kararraki da sharhi da ke cike da bakar manufa da nufin haifar da fitina a cikin gida da kuma dushe hasken zaben a wajen kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, daga cikin hanyoyin da wadannan kafafen watsa labaran suke bi wajen cimma wannan bakar aniya ta su, sun hada da goyon bayan wani ko kuma wasu ‘yan takaran zaben da kuma bata sunan sauran, wanda ko shakka babu manufar hakan ita ce haifar da rikici tsakanin al’ummar ta Iran da kuma kokarin hana su fitowa kada kuri’unsu a lokacin zaben. Daya daga cikin hanyoyin da kafafen watsa labaran na yammaci suka so bi wajen haifar da fitinar cikin gidan ita ce matsayar da sauran ‘yan takaran da ba a tantance su da kuma amincewa da bukatar tsayawa takarar da suka yi za su dauka.
A tunaninsu wadannan ‘yan takaran za su yi fito na fito da gwamnatin matukar dai ba a tantance sunayen na su ba, to amma matsayar da suka dauka da girmama doka da kuma kiran jama’a da su fito zaben da wadannan mutanen suka yi, hakan ya kashe musu gwiwa da kuma bakanta musu rai matuka.
Da dama daga cikin ‘yan siyasan Iran cikinsu kuwa har da ‘yan takaran da ba a tantance sunayen na su ba sun yi amanna da cewa babbar abin da kafafen watsa labaran kasashen yammacin suka sa a gaba shi ne bakanta al’ummar Iran da kuma tsarin Musulunci da ke mulki a kasar a idon duniya. A saboda haka ne ba su dauke su a matsayin abin yarda ba duk kuwa da kokarin nuna kansu a matsayin masu kaunar al’ummar Iran din da suke yi.
Yayin da ya ke magana kan hakan, Sayyid Husain Naqwa Husaini, kakakin kwamitin tsaron kasa da siyasar kasashen waje na majalisar shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewar babu yadda za a yi kafafen watsa labaran kasashen waje su zamnto tushen samun labaran al’ummar Iran, don kuwa a koda yaushe sun kasance masu shafa baken fenti da kuma barazana ga manufofin al’ummar Iran ne. Dan majalisar ya ci gaba da cewa: Tsawon tarihi a duk lokacin zabe kafafen watsa labaran kasashen yammaci sun kasance masu kokari wajen haifar da fitina ne tsakanin al’ummar Iran, don haka babu yadda za a yi al’ummar Iran su amince da abubuwan da suke fadi.
Shi ma a nasa bangaren shugaban kwamitin hakkoki da shari’a na majalisar shawarar Musulunci ta Iran din Allahyar Malek Shahi cewa ya yi al’ummar Iran dai al’umma ce ma’abociyar tunani da kuma fahimta, don haka duk wata farfaganda da kafafen watsa labaran kasashen yammacin za su yi, ba za ta yi musu tasiri ba, don kuwa sun san cewa babu gaskiya ko alheri cikin abubuwan da suke fadi, don haka ko da wasa ba za su yi nasara ba kamar yadda a baya ma ba su yi nasarar ba.
Dubi cikin ayyukan kafafen watsa labaran kasashen waje a duk lokacin zabe a kasar iran, musamman ma lokacin zaben shugaban kasar, a fili za a iya fahimtar cewa babban abin da kafafen watsa labaran kasashen yammacin da masu su suka sa a gaba shi ne sanya rashin yarda, kashe gwiwan mutane, nuna akwai tazara mai girma tsakanin al’umma da tsarin Musulunci, bugu da kari kan sanya shakku cikin zukatan mutane kan cewa babu bukatar su fito zaben don kuwa tuni an riga da an tsara komai. To sai dai kuma irin fitowar da al’ummar Iran suke yi a duk lokacin zaben yana nuni da cewa dukkanin wannan kokari da ayyuka na makiyan ya zamanto aikin baban giwa.

1238782





captcha