IQNA

'Yan Takara Neman shugabancin Kasa Sun Kammala Yakin neman Zabe A Iran

17:42 - June 13, 2013
Lambar Labari: 2546650
Bangaren siyasa, a daren jiya ne dukkanin 'yan takarar shugabancin kasar Iran 6 suka kawo karshen yaki neman zabe a fadin kasar, wanda za a gudanar gobe Juma'a 14 ga watan Yuni, tare da halartar daruruwan masu sanya ido da kuma manema labarai daga kasashen duniya daban-daban.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa dukkanin 'yan takarar sun gudanar da yakin neman zabe lafiya a fadin kasar ta Iran ba tare da fuskantar wani tashin hankali tsakanin magoya bayan 'yan takarar ba, haka nan dukaknin 'yan takarar sun ja hankulan magoya bayansu da su zama masu kiyaye doka da oda, da kuma kiyaye hakkokin jama'a, domin kuwa manufar kowane dan takara ita ce yi al'ummar kasarsa hidima.

A gobe ne da kimanin karfe 8 agogon Tehran za a bude runfunan zabe a dukkanin fadin kasar, kimanin Iraniyawa miliyan 50.5 ne dai suka cancanci kada kuri'a a kasar, kuma ana sa ran fiye da kashi 70% na wadanda suka cancanci kada kuri'ar ne za su kada kuri'unsu a gobe.

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran kana kuma daya daga cikin ‘yan takaran shugabancin kasar Dakta Sa’id Jalili ya bayyana cewar matukar aka zabe shi a matsayin shugaban kasar to babu wani sassauci da Iran za ta yi a gaban kasashen yammaci dangane da shirin nukiliyanta na zaman lafiya.
Dakta Jalili, wanda yake kan gaba-gaba a tsakanin sauran ‘yan takaran, ya bayyana hakan ne a jiya a lokacin da yake gabatar da jawabi a garin Arak na kasar ta Iran inda ya ce watsi da wannan shiri na nukiliya tamkar watsi ne da asalin kasantuwar kasar Iran inda ya kirayi al’ummar Iran din da kada su bari barazana da takunkumi sun sanya su yin sako-sako da wannan hakki na su.
A yau ne ake sa ran ‘yan takaran shugabancin na Iran su takwas za su gudanar da muhawara ta sa’oi hudu a tsakaninsu kan shirye-shiryen da suke da shi a fagen tattalin arziki da gidan talabijin din kasar zai watsa kai tsaye.
A ranar 14 ga watan Yuni mai kamawa ne ake sa ran za a gudanar da zaben shugaban kasar na Iran don zaban shugaban da zai maye gurbin shugaban kasar na yanzu Dakta Mahmud Ahmadinejad wanda wa’adin mulkinsa zai kare bayan zaben.
1241971




captcha