Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, A nasa bangaren ministan harkokin cikin gida Mustafa Muhammad najjar ya bayyana cewa, tun kafin lokacin fara zaben miliyoyin mutane suka fita domin kada kuri'unsu, lamarin da ke tabbatar da cewa al'ummar kasar sun fita kwansu da kwarkwatarsu domin gudanar da wannan zabe, Najjar ya kara da cewa da rana an kammala kada kuri'un ba tare da wani bata lokaci ba za a fara kidayar su.
Ma'aikatar harkokin cikin gida akasar Iran ta bayyana cewa ana ci gaba da kidaya dukkanin kuri'un da aka kada a jiya a zaben shugaban kasa da na kananan hukumomi.
A wani taron manema labarai da ya gudanar dazu-dazunnan, ministan harkokin cikin gida na kasar Iran Mustafa Najjar ya bayyana cewa, an kirga kuri'u miliyan 16, 716, 937, kuma Hassan Rauhani shi ne kan gaba, ya ce ana sa ran kammala kidaya dukaknin kuri'un ne a cikin daren yau.
Da dama daga cikin masu sanya ido daga kasashen duniya da kuma manema labarai na kasashen ketare suna ci gaba da bin kadun abubuwan da ake ciki na kidaya kuri'un, yayain da sauran mutane suke jiran su ji sakamako na karshe.
1243091