IQNA

Ana Ci Gaba Da taya Sabon Shugaban kasar Iran Murna daga kasashen duniya

18:02 - June 16, 2013
Lambar Labari: 2547997
Bangaren siyasa, babban sakataren majalisar dinkin duniya ya aike da sakon taya murna ga zababben shugaban kasar Iran Dr. Hassan rauhani, tare da bayyana cewa majalisar dinkin duniya za ta ci gaba da yin aiki tare da Iran a cikin lamurra da suka shafi yankin gabas ta tsakiya da ma sauran batutuwa na kasa da kasa.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Mai magana da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Martin Nesirky ya bayyana cewa, Ban Ki Moon na da aniyar yin aiki tare da sabon shugaban kasar Iran a kan batutuwa da dama, tare da bayyana cewa Ban Ki Moon ya gamsu matuka dangane da yadda al'ummar Iran suka gudanar da zaben lami lafiya, budu da kari kan hakan kuma adadin wadanda suka kada kuri'a ya kai kashi 72%.

Rauhani ya lashe zaben shugaban kasa karo na 11 da aka gudanar a kasar Iran ne a ranar Juma'ar da ta gabata da kashi 50.68% na dukkanin kuri'un da aka kada, wanda hakan ya ba shi damar zama zababben shugaban kasa na 7 a kasar, tun bayan samun nasarar juyin juya halin musulunci a shekara ta 1979.

Rauhani ya mika godiya ta musamman ga jagoran juyin juya halin muslunci na kasar Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, tare da sauran malaman addini da kuma masana daga bangarori daban-daban na kasar, inda su ne taka rawa matuka wajen sanya fata a cikin zukatan al'ummar kasar Iran, tare da karfafa gwiwarsu wajen nuna wa duniya cewa Iran kasa da al'umma suke da 'yanci wajen zabar makomarsu.

1243651






captcha