IQNA

Bayani sun tabbatar da cewa mutanen da suka kashe 'yan shi'a a Masar an san su

17:52 - June 25, 2013
Lambar Labari: 2552095
Bangaren kasa da kasa, wasu bayanai daga bangarorin shari'a da kuma na watsa labarai a kasar Masar sun tabbatar da cewa mutanen da suka kai hari mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a kasar a ranar lahadi da ta gabata an san su kuma suna daurin gindi daga mahukuntan kasar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ahram cewa, bayanai daga bangarorin shari'a da kuma na watsa labarai a kasar Masar sun tabbatar da cewa mutanen da suka kai hari mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a kasar a ranar lahadi da ta gabata an san su kuma suna daurin gindi daga mahukuntan kasar.

Malamai da dama da kungiyoyin kare hakkin bil adama sun fitar da bayanai na yin Allawadai da kisan gillar da wasu 'yan salafiya Takfiriyyah suka yi wa malami a jami'ar Azhar Shekh Hassan Shuhhat saboda bambancin Mazhaba, yayin da jami'ar ta Azhar ta bayyana hakan da cewa yana daga manyan zubbbai (kaba'ira) da aka aikata a tarihin kasar Masar.

Shi kuwa madugun adawa na kasar Muhammad Barade'i ya ce wannan wani sabon abu ne mai matukar hadari da al'ummar kasar Masar suka fara gani sakamakon salon mulkin da ke tafiyar da kasar a halin yanzu. A nasa bangaren babban mai shigar da kara na kasar Masar Tal'at Ibrahim ya bayar da umurnin gudanar da binciken gaggawa kan wannan aiki da ya ce ya faru a gaban jami'an 'yan sanda, tare da kame duk wani wanda ake zargin yana da hannu cikin lamarin ba tare da wani bata lokaci ba.

1247718




















captcha