IQNA

Ana ci gaba da sukar mahukuntan kasar Masar kan kisan malamin shi'a

23:56 - June 29, 2013
Lambar Labari: 2553669
Bangaren kasa da kasa, ana ci gaba da sukar mahukutan masar kan kisan shehin malaimin shi'a Hassan Shehhat wanda a ka yi karkashin m7ulkin Morsi wanda ya nuna matukar adawarsa da mazhabar iyalan gidan amnzon Allah a kasar.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa,a ci gaba da nuna adawa da gwamnatin kasar a birnin Alkahira dubban magoya bayan Mohammad Morsi sun taru ne a masallacin Rabi'at Adwiyyah, inda suka yi ta rera taken nuna goyon bayansu gare shi, tare da sukar masu adawa da shi, yayin da dubban masu adawa da Morsin kuma suka taru a dandalin Tahrir, wasu kuma suka taru a kofar fadar shugaban kasa da ke yankin Ittihadiyyaha cikin birnin na Alkahira, inda suke kira ga Morsi da ya gaggauta safka.

Domin abin da suka kira gazawarsa a dukkanin bangarori tun bayan da ya karbi shugabancin kasa shekara guda da ta gabata, tare da killace mukamai da dukakin harkokin gudanarwa a kasar ga 'yan kungiyar 'yan uawa musulmi kawai, sauran mutane kuma sun zama 'yan kallo, yayin da wasunsu kuma suke bayyana Morsi da kungiyar 'yan uwa musulmi a matsayin wadanda suka sace juyin juya halin da al'ummar kasar suka yi a kan gwamnatin Husni Mubarak, inda Morsi da kungiyarsa suka kafa wata gwamnatin da bata da bambanci da ta Husni Mubarak.

A birnin Iskandariya kuwa, dubban mutane ne suka kai farmaki kan ofishin kungiyar 'yan uwa musulmi ta Muhammad Morsi, inda suka banka masa wuta, biyo bayan wata taho mu gama da aka yi tsakanin 'yan kungiyar ta 'yan uwa musulmi da kuma masu adawa da Muhammad Morsi a garin na Iskandariya, babban jami'in 'yan sanda na birnin ya ce wani ba'amuke ya rasa a yayin gumurzun a lokacin da yake daukar hotuna, ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta tabbatar da wannan labari, inda ta bukaci jami'an huldar diplomasiyyarta da ke kasar da ayyukansu ba su zama dole ba, da su bar kasar, kamar yadda ta bukaci Amurka da ke nufin yin tafiya zuwa Masar da su dakata.

1249208


captcha