Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, duk kuwa da cewa daga bisani a cikin bayaninsa nasa ya kiraye su zuwa ga tattaunawa, amma bangarorin adawar sun yi watsi da wannan tayi nasa, tare da bayyana hakan a matsayin wani shure-shure ne da Morsi ke yi, domin kuwa a cewarsu a gobe Lahadi za su gudanar da wata zanga-zanga mafi girma a kasar, wadda za ta kai ga kifar da gwamnatinsa, daga bayan gabatar da jawabin Morsia daren Laraba zuwa safiyar yau Asabar, mutane 7 ne suka rasa rayukansu, wasu fiye da 500 kuma suka samu raunuka sakamakon rikicin da ya biyo bayan jawabin nasa.
Ko shakka babu abin da yake faruwa a kasar ta Masar a halin yanzu ba bushara ce ta alkhari ga makomar kasar ba, musamman ma idan aka yi la'akari da yadda 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi da kuma wasu daga cikin 'yan salafiyya na kasar suka tsaya kai da fata tare da gindaya rayuwarsu a kan cewa ba za su taba amincewa da duk wani mulki in ban a Morsi ba,
A daya bangaren kuma masu adawa da magoya bayansu suka tsaya kai da fata a kan cewa dole sai Morsi ya safka domin gudanar da wani zabe na gaggawa, kuma ga dukkanin alamu ba daya daga cikin bangarorin biyu da yake shirye domin yin sassuci kan matsayinsa.
1249151