Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto ana shafin sadarwa na yanar gizo cewa, ana ci gaba da an nuna damuwa matuka dangane da halin da ake ciki na rashin tabbas a kasar Masar bayan da al'ummar kasar suka motsa domin kifar da gwamnatin Morsi wanda ya gaza aiwatar da komai tsawon shekara guda yana kan karagar mulki.
A ci gaba na zanga-zangar neman kifar da Gwamnatin Mursi a kasar Masar wasu Ministoci guda hudu sun yi murabus don kawo goyan bayansu ga ‘yan adawa.
Mininstocin sun hada da Ministan harkokin shara’a , ministan yawon bode ido,Ministan watsa labarai da Ministan kare mahalli.
Daga bangare guda wasu labarai sun habarta cewa Minista mai kula da al’amuran Majalisa shima ya mika takardar murabus kinsa ga Gwamnatin kasar amma har yanzu Gwamnati bata amince da bukatar tasa.
Zanga-zangar ta shiga rana ta biyu tun bayan da ‘yan adawa suka taru a Dandalin tahrin a jiya lahadi ranar cikon shekara guda da rantsuwar Muhamad Mursi na kama milki a kasar.
1250815