Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, tun a ranar Lahadi da ta gabata ce miliyoyin mutanen kasar suka fara gudanar da zanga-zanga da aka ce ita ce mafi girma a tarihin kasar Masar, domin nuna adawa ga shugaban kasar Muhammad Morsi, tare da kiransa da ya safka daga kan karagar shugabancin kasar.
Ana gudanar da zanga-zangar ne a dukkanin biranan kasar ta Masar, inda aka cika dukkanin wuraren taruka na mayan birane musamman ma dandalin Tahrir da kuma yankin Ittihadiyya da ke kusa da fadar shugaban kasa a birnin Alkahira, miliyoyon masu zanga-zanga sun cika wuraren suna rera taken kira ga Morsi da ya safka.
A daya bangaren wasu daga cikin magoya bayan Morsi sun taru a masallacin Rabi'at Adwiyyah da ke birnin Alkahira domin nuna goyon bayansu, rahotanni sun ce an kashe masu adawa da Morsi 5 a ranar Lahadi a biranan Asyut, Afyum da kuma Alkahira yayin da wasu kimanin 200 suka samu raunuka.
Rundunar sojin kasar Masar dai ta ce tana bin diddigin abin da ke gudana, kuma za ta dauki matakan da suka dace matukar dai suka ga kasar za ta shiga wani hali na yakin basasa.
1251747