IQNA

An Gudanar Da Zanga-Zangar Nuna Bacin Rai Game Da Sumaman Da Jami'an Tsaro Suka Kai A Bahrain

0:02 - July 04, 2013
Lambar Labari: 2556184
Bangaren kasa da kasa, Al’ummar Bahrain sun gudanar da zanga-zanga don nuna bacin ransu kan wani samame da Jami’an tsaron kasar suka kai a gidan babban malamin nan Dan shi’a Sheik Isa Kasim.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya juma’a da safe Jami’an tsaron suka kai samame a gidan Babban malamin nan Dan Shi’a Sheik Isa Kassim, a yayin da suka je gidansa basu samu babban malamin a gida amma sun kuble iyalansa cikin wani daki inda su kayi gaggaran bincike a gidan sannan sun ba ta abubuwa da dama a gidan
A kwanakin baya ma Gwamnati tayi barazanar kashe wannan babban malamin.
Al’ummar kasar Bahrai taja kunnan Gwamnati da kadda ta sake irin wannan cin mutunci ga wannan babban malami inda tace duk abinda ya samu wannan malami to alhakinsa na wuyan Gwamnatin.
Kungiyar malaman musulmi na kasar Labanon sun yi Allah wadai da matakin da gwamnatin Al Khalifa ta kasar Bahrain ta dauka na rusa masallatai da kuma wajaje masu tsarki da suke yi a kasar da nufin kawo karshen boren neman sauyi da al’ummar kasar suke yi.
Tashar talabijin din Al-Alam da ke watsa shirye-shiryensa daga nan Tehran a cikin wata sanarwa da kungiyar malaman ta fitar a yau din nan laraba ta bayyana cewar: abin da a halin yanzu yake faruwa a kasar Bahrain wani makirci ga addinin musulunci da kuma dukkanin mazhabobi wanda ba ya halalta a ci gaba da zuba ido ana ganin hakan na faruwa.
Har ila yau kuma yayin da suke ishara da irin take hakkokin al’ummar Bahrain da gwamnatin kasar take yi, malaman sun bayyana wajibcin kiyaye hakkokin al’ummomin ba tare da nuna wani bambanci na mazhaba ko kabila ba.
A cikin ‘yan kwanakin nan dai mahukuntar kasar Bahrain din sun matsa kaimi wajen ci gaba da zaluntar al’ummar kasar da suka mike don neman hakkokinsu da aka take da kuma rusa masallatai da sauran wajaje masu tsarki na wadannan al’ummomin.

1251389




captcha