Bangren kasa da kasa, masarautar kasar Bahrain na ci gaba da fallazawa mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a kasar da sunan yaki da masu tayar da hankali ko kuma yi ma masaraurtta bore wanda hakan ya kais u ga daure kananan yara da shekarunsu ab kai ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa masarautar kasar Bahrain na ci gaba da fallazawa mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a kasar da sunan yaki da masu tayar da hankali ko kuma yi ma masaraurtta bore wanda hakan ya kais u ga daure kananan yara da shekarunsu bas u kai na dauri ba a kasar.
Al’ummar Bahrain sun gudanar da zanga-zanga don nuna bacin ransu kan wani samame da Jami’an tsaron kasar suka kai a gidan babban malamin nan Dan shi’a Sheik Isa Kasim. A jiya juma’a da safe Jami’an tsaron suka kai samame a gidan Babban malamin nan Dan Shi’a Sheik Isa Kassim, a yayin da suka je gidansa basu samu babban malamin a gida amma sun kuble iyalansa cikin wani daki inda su kayi gaggaran bincike a gidan sannan sun ba ta abubuwa da dama a gidan
A kwanakin baya ma Gwamnati tayi barazanar kashe wannan babban malamin. al’ummar kasar Bahrai taja kunnan Gwamnati da kadda ta sake irin wannan cin mutunci ga wannan babban malami inda tace duk abinda ya samu wannan malami to alhakinsa na wuyan Gwamnatin.
1252167