IQNA

An bude wani gidan radio da talabijin a birnin Beirut na musulunci

22:45 - July 05, 2013
Lambar Labari: 2556531
Bangaren kasa da kasa, an bude wani gidan radiyo da talabijin wanda zai rika watsa shirin muslunci karkashin klawar gwagwarmayar kasar da kuma taimakon wasu daga cikin kasashen mabiya tafarkin iyalan gidan manzo da ke yankin.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya an bude wani gidan radiyo da talabijin wanda zai rika watsa shirin muslunci karkashin klawar gwagwarmayar kasar da kuma taimakon wasu daga cikin kasashen mabiya tafarkin iyalan gidan manzo da ke yankin, musamman ma jamhuriyar muslunci.
A bangare guda kuma kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta yi kakkausar suka ga kalaman ministan harkokin wajen kasar Saudiyya Sa’ud Faisal na cewa kungiyar da kuma kasar Iran sun mamaye kasar Siriya inda tace hakan wani kokari ne kawai na wasa da hankalin mutane da mahukuntan Saudiyyan suke yi.
Kungiyar ta bakin daya daga daya daga cikin membobinta a majalisar dokokin kasar Labanon Ali Fayyaz ya bayyana cewar: Abin da ya kamata Saudiyyan ta yi shi ne ta dakatar da aikewa da makamai da kudade zuwa ga ‘yan ta’addan da suke haifar da fitina a kasar Siriyan ta riki tafarki na siyasa wajen magance rikicin kasar Siriyan. Ali Fayyaz ya kara da cewa kasar Iran da kuma kungiyar Hizbullah suna fatan ganin an magance matsalar kasar Siriya ne ta hanyar siyasa da tattaunawa tsakanin al’ummar kasar.
A shekaran jiya ne dai ministan harkokin wajen kasar Saudiyyan, a wata ganawa da ya yi da manema labarai da takwaransa na kasar Amurka John Kerry ya bayyana cewa kungiyar Hizbullah da kasar Iran sun mamaye kasar Siriya yana mai kiransu da su fice daga kasar, lamarin da masana da masu sharhi daban-daban suka yi watsi da shi bisa la’akari da hannun da Saudiyya take da shi cikin kirkira da kuma ci gaba da ruruta wutar rikicin kasar Siriya ta hanyar goyon baya da kuma ba wa ‘yan ta’adda makaman da suke ci gaba da kashe al’ummar kasar Siriyan.

1252181



captcha