Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a daren jiya laraba ce ministan tsaro kuma babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Janar Abdul Fattah Al-Sisi, wanda wasu jagororin addini da na ‘yan adawa suke rufa masa baya, ya sanar da kifar da gwamnatin Morsin da kuma gabatar da wata taswirar hanya wacce za a bi a wajen gudanar da makomar kasar.
A cikin sanarwar, Janar Sisin ya bayyana cewar: A zaman da kungiyoyin ‘yan siyasa na kasar Masar suka yi da kwamandojin soji kan makomar kasar Masar, sun cimma wata taswirar hanya wacce ta kumshi cewa: za a dakatar da kundin tsarin mulkin na yanzu da kuma kafa wani kwamiti da zai kumshi dukkanin bangarorin ‘yan siyasa wajen yi masa kwaskwarima. Haka nan kuma an nada shugaban kotun koli mai kula da kundin tsarin mulki a matsayin shugaban kasa wanda zai yi rantsuwar kama aiki a gaban kotun kula da kundin tsarin mulkin.
Har ila yau kuma bisa wannan taswirar hanyar, za a gudanar da zabubbukan shugaban kasa da na ‘yan majalisa cikin gaggawa, kamar yadda kuma aka ba wa sabon shugaban cikakken ikon gudanar da kasar.
Bayan jawabin babban hafsan hafsoshin, wasu daga cikin malaman addini da ‘yan siyasar kasar da suka amince da sauke shugaba Morsin sun gabatar da jawabai da kuma dalilansu na amincewa da hakan.
A nasa bangaren shugaban jami’ar Al-Azhar Sheikh Ahmad Tayyib ya bayyana amincewarsa da matakin da aka daukan inda ya yi kira da a gudanar da zaben cikin gaggawa. Haka nan shi ma a nasa bangaren shugaban Cocin Kifdawa na kasar Paparoma Tawadros na 2 shi ma ya sanar da amincewarsa da matakin da aka daukan kamar yadda su ma ‘yan Salafiyya na kasar karkashin jam’iyyar Al-Nur suka sanar da amincewarsu saboda abin da suka kira kare zubar da jinin al’ummar Masar. Shi kuwa Muhammad Baradei, wakilin jam’iyyun adawa a wajen tattaunawa da sojojin, bayan bayyanar da amincewarsu da matakin da sojojin suka dauka, ya sanar da cewa taswirar hanyar da aka cimma za ta lamunce gudanar da ingantaccen zabe cikin gaggawa a kasar.
1252398