IQNA

Wasu Rahotanni Sun Ce An Kame Shugaban 'Yan uwa Musulmi

15:17 - July 06, 2013
Lambar Labari: 2556553
Bangaren kasa da kasa, wasu rahotanni sun ce an kame shugaban kungiyar 'yan uwa musulmi, amma daga bisani ya bayyana a gaban magoya bayan kungiyar a yaua a birnin Alkahira na kasar ta Masar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Jagoran kungiyar 'yan uwa musulmi a kasar Masar Muhamamd Badi ya bayyana cewa, za su ci gaba da yin zaman dirshan kan tituna har sai an dawo da Muhammad Morsi a matsayin shugaban kasa.

Muhammad Badi ya bayyana hakan ne a gaban dubban magoya bayan kungiyarsa da suka yi cincirindo a masallacin rabi'at adwiyyah da ke birnin Alkahira, inda ya ce ba za su taba amincewa da abin da ya kira juyin mulkin sojoji kan Morsi ba, kuma harsasan bindiga da tankokin yaki ba za su tsorata su ba, ya ce a shirye suke su fahimci juna tare da sojoji idan har suka mayar da Morsi kan shugabancin Masar.

Mutane uku ne dai aka tabbatar da sun rasa rayukansu a yau a taho mu gamar da aka yi tsakanin magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi da kuma 'yan adawa a cikin birnin Alkahira, kamar yadda wasu da dama kuma suka samu raunuka.

Muhammad Badi ya musunta rahotannin da ke cewa jami'an tsaro sun yi awon gaba da shi tare da tsare shi a gidan kaso.

1252603









captcha