IQNA

Ana ci gaba da dambarwar siyasa a Masar tun bayan kifar da Morsi

0:03 - July 08, 2013
Lambar Labari: 2557828
Bangaren kasa da kasa, kakakin shugaban rikon kwarya na kasa Masar Ahmad Musalmani ya bayyana cewa an gabatar da sunaye domin zabar firayi minista da zai jagoranci majalisar ministoci a kasar da suka hada da Muhammad Albaradei, amma har yanzu ba a cimma matsaya kan hakan ba.
Kamfanin dilalncin labarabn iqna ya habarta cewa, a jiya kakakin shugaban rikon kwarya na kasa Masar Ahmad Musalmani ya bayyana cewa an gabatar da sunaye domin zabar firayi minista da zai jagoranci majalisar ministoci a kasar da suka hada da Muhammad Albaradei, amma har yanzu ba a cimma matsaya kan hakan ba kamar dai yadda ya fada.

Musalmani ya ce Muhammad Albaradei ne kan gaba daga cikin wadanda aka gabatar da sunayensu, amma har yanzu ba a yanke shawara guda ba kan wanda zai rike wannan mukami a tsakanin 'yan takarar, amma dai ana ci gaba da tattauna batun tsakanin bangarorin siyasa.

Matasan da suka jagorancin gagarumar zanga-zangar da ta kai ga kifar da gwamnatin Morsi ne suka bayar da sunan Muhammad Albaradei a matsayin dan takararsu domin rike mukamin firaministan rikon kwarya, amma jam'iyyar Nur ta 'yan salafiyyah wadda ita ta goyi bayan kifar da Morsi, taki amince da zabar Muhammad Baradei, wanda ake ganin shi ne ya fi samun karbuwa a tsakanin matasan kasar Masar a halin yanzu.

1253694








captcha