Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ce wasu daga cikin masana sun yi iamnin cewa, babbar jami'ar Azahar ta nuna halin ko in kulak an abin da yake faruwa kan mabiya tafarkin iyalan gidan amnzo a masar a lokacin da aka dfara fuskantar rikicin siuasa da kuma kafirta musulmi a kasar sakamakon siyasar Morsi a kasar.
Kungiyar matasan gugun 30 ga watan Yuni da shirya zanga-zangar adawa da Muhammad Morsi ta sake kiran wata zanga-zangar a yau a dukkanin fadin kasar Masar, domin tabbatar da abin da suka kira juyin juya hali na biyu a kasar wanda ya kifar da gwamnatin Muhammad Morsi.
Wannan kira da kungiyar matasan ta yi dai ya zo ne a daidai lokacin da magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi suke ci gaba da gudanar da gangami a gaban masallacin Rabi'at Adwiyyah da ke birnin Alkahira, da ma wasu biranan kasar, domin nuna rashin amincewarsu da kifar da gwamnatin Morsi, tare da neman a dawo da shi kan mulki.
Da dama daga cikin jagororin kungiyar matasan 30 ga watan Yuni dai su ne suka jagoranci boren da ya kai ga kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Masar Muhammad Husni Mubarak a cikin watan Fabrairun shekara ta 2011, wanda hakan ne ya baiwa kungiyar 'yan uwa musulmi da aka haramta a kasar tsawon shekaru damar dawowa a fagen siyasa, har ta samu shugabancin kasar ta Masar, bayan shudewar shekara guda matasan sun sake tayar da boren kiyayya da gwamnatin Morsi wanda hakan ya kai kifar da gwamnatin 'yan uwa musulmi a ranar 3 ga wannan wata na Yuli.
1253766