IQNA

Jami'ar Azahar ta nuna damuwa kan halin da ake ciki a kasar Masar

0:02 - July 10, 2013
Lambar Labari: 2559134
Bangaren kasa da kasa, bababr jami'ar muslunci ta kasa Masar ta Azhar ta nuna damuwa matuka dangane da halin da ake ciki inda da jijjifin safiyar Ltinin din da ta gabata ce wasu daga cikin magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi ta Muhammad Morsi hambararren shugaban kasar ta Masar suka kai farmaki kan wani babban magini na ma'akatar tsaron kasar da ke birnin Alkahira,


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ana zaton cewa a nan ne ake tsare da Morsi, inda suka yi ba-ta-kashi tsakaninsu da sojojin da ke gadin wurin, lamain da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 42 daga cikin 'yan kungiyar ta 'yan uwa musulmi a wannan artabu, kamar yadda wani babban jami'in soji da kuma karami soji suka rasa rayukansu, wasu sojojinfiye da 40 suka samu munanan raunuka.

'Yan sa'oi bayan faruwar lamarin rundunar sojin ta Masar ta bayyana cewa magoya bayan Morsi da suka kawo farmaki a wrin suna dauke da makamai ne, kamar yadda sojojin suka nuna hotunan bidiyo da kamarori suka dauka a wurin, da ke nuna wasu daga cikin magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi dauke da makamai a lokacin da suka kawo farmakin. Bayanin rundunar sojin ya ce an kame wasu mutane 200 daga cikinsu da suke dauke da makamai.

Bangarori daban-daban da suka hada majalisar dinin duniya da kuma bababr jami'ar muslunci ta Azahar gami da bangarorin adawa a kasar, sun bukaci da a gudanar da bincike kan hakikanin abin da ya faru, domin hukunta duk wanda aka samu da laifi kan lamarin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 42 a nan take, adadin da ya karu daga bisa zuwa hamsin da biyu.

1254922





captcha