Bangaren kasa da kasa, kungiyar yan uwa musulmi a kasar tana hankoron ganin ta dawo ad martabar da samu a lokutan baya wadda ta zube a halin yanu a gaban al'ummar kasar da ma sauran al'ummomin duniya sakamakon kurakuran siyasa da suka yi ta tafkawa.
Kamfanin dilalcin labaran iqna ya habarta cewa, magoya bayan hambararren shugaban kasar suna ci gaba da yin zaman dirshan masallacin Rabi'ar Adwiyyah da ke birnin Alkahira, da zimmar cewa ba za su taba barin wurin ba har sai an dawo da Muhammad Morsi kan kujerarsa.
A nasu bangaren kuwa matasan gungun 30 ga watan Yuni da suka shirya zanga-zangar da ta kai ga kifar da Muhammad Morsi bayan da sojoji suka shiga cikin lamarin, sun yi kira da a kame wasu daga cikin jagororin kungiyar 'yan uwa musumi, bayan abin da suka kira daukar makamai da kuma kai hari kan sojoji da 'yan sanda da 'yan kungiyar suka yi.
Da dama daga cikin jagororin kungiyar matasan 30 ga watan Yuni dai su ne suka jagoranci boren da ya kai ga kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Masar Muhammad Husni Mubarak a cikin watan Fabrairun shekara ta 2011, wanda hakan ne ya baiwa kungiyar 'yan uwa musulmi da aka haramta a kasar tsawon shekaru damar dawowa a fagen siyasa, har ta samu shugabancin kasar ta Masar, bayan shudewar shekara guda matasan sun sake tayar da boren kiyayya da gwamnatin Morsi wanda hakan ya kai kifar da gwamnatin 'yan uwa musulmi a ranar 3 ga wannan wata na Yuli..
1255289