IQNA

Rashin bin koyarwar kur'ani mai tsarki babban dalilin faduwar Morsi

10:11 - July 13, 2013
Lambar Labari: 2559954
Bangaren kasa da kasa, wani masani kan harkokin siyasar kasashen larabawa kuma mai sharhi kan abubuwan da suke da komowa acikin wadannan kasashe ya bayyana cewa rashin bin sahihin tafarki da koyarwar kur'ani mai tsarki su ne dalilan faduwar Morsi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Hujjatollah Judi wani masani kan harkokin siyasar kasashen larabawa kuma mai sharhi kan abubuwan da suke da komowa a cikin wadannan kasashe ya bayyana cewa, rashin bin sahihin tafarki da koyarwar kur'ani mai tsarki su ne dalilan faduwar shugaban kasar Masar da aka hambarar.
Rikici na kara kamari a kasar Masar tun dai bayan da sojoji suka kifarda gwamnatin Shugaba Mohamed morsi, inda kungiyar 'yan misilmi mai goyan bayan hambararen shugaban ta shiga wani yanayi na kadamarda zanga-zanga a duk fadin kasar domin nuna adawa da juyin mulkin da soja suka yi a kasar.
Rahotanni daga kasar na nuni da cewa akala mutane 26 ne suka ratsa rayukan yayinda wasu daruruwa kuma suka sami raunuka sakamakon rikicin da ya barke a jiya Juma’a tsakanin magoya baya hambararen shugaban da masu adawa da shi. A hanu daya kuma jagoran kungiyar 'yan uwa musulmi a kasar Masar Muhamamd Badi ya bayyana cewa, za su ci gaba da yin zaman dirshan kan tituna har sai an dawo da Muhammad Morsi a matsayin shugaban kasa.
Muhammad Badi ya bayyana hakan ne a gaban dubban magoya bayan kungiyarsa da suka yi cincirindo a masallacin rabi'at adwiyyah da ke birnin Alkahira, inda ya ce ba za su taba amincewa da abin da ya kira juyin mulkin sojoji kan Morsi ba, kuma harsasan bindiga da tankokin yaki ba za su tsorata su ba, ya ce a shirye suke su fahimci juna tare da sojoji idan har suka mayar da Morsi kan shugabancin Masar haka kuma Muhammad Badi ya musunta rahotannin da ke cewa jami'an tsaro sun yi awon gaba da shi tare da tsare shi a gidan kaso.
A wani labari kuma Kungiyar tarayyar kasashen Afirka (AU) ta bayar da sanarwa a ranar jiyya Jumma'a na dakatar da kasar Masar din daga cikin kungiyar bayan hambarar da Mohmammed Morsi daga mukamin shugaban kasar da sojoji suka yi. A cikin wata sanarwar da ta bayar, hukumar kungiyar AU mai kula da harkokin zaman lafiya da tsaro, ta ce ta dakatar da kasar ta Masar da ke arewacin Afirka daga dukkan ayyukan kungiyar don matsa lambar ganin an dawo da doka a kasar.
A nasu banagare kwa Sojoji a kasar ta Masar sun fitarda wata sanarwa kan kiran sasantawa ta kasa, bayan da suka kifarda gwamnatin shugaba Morsi a ranar Laraba. Sanarwar na zuwa ne bayan da kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Mohamma Morsi ta yi kiran da a fito a ci gaba da gudanar da zanga-zangar lumana a a duk fadin kasar kana kuma kungiyar ta yi watsi da tayin da shugaban kasa na riko Adly Mansour yayi musu na su shiga cikin gwamnatin hadin kan kasa.
A nata banagare Heba Morayef daraktar Kungiyar kare hakkin bil Adama ta 'Human Rights Watch' a kasar Masar, ta shaida cewa wannan wani hali na bakin ciki ne ga dimokradiyyar kasar ta Masar. Uwaglgida Morayef ta ce hakan ya kawo koma baya ga cigaban dimokradiyyar kasar, kana ya jefa tsaren sauya gwamnati cikin hadari, Inda ta kara da cewa matakin da sojin suka dauka a cikin sa'oi 24 da suka gabata, na kame da kuma rufe tashohin yada labarai, zai durkusar da al'amuran kasar.
1255952



captcha