Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin musuluncia kasar Amurka suna kokarin ganin sun hada kan mabiya addinai daban-daban a kasar a cikin watan Ramadan watan albarka da daraja da rahmar ubangiji kamar yadda sauran takwarorinsu na sauran kasashen turai ke kokarin yi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, mabiya addinin musuluncia kasar Amurka suna kokarin ganin sun hada kan mabiya addinai daban-daban a kasar a cikin watan Ramadan watan albarka da daraja da rahmar ubangiji kamar yadda sauran takwarorinsu na sauran kasashen turai ke kokarin yi a cikin wannan wata.
A cikin mabiya addinin musulunci a kasar faransa suna ciyar da mabukata a lokacin buda baki a masallatai daban-daban na kasar Faransa a matsayin daya daga cikin kyawawan ayyuka da muslunci ya umurni da su kasantuwar muslunci a ddini ne na jin kai da kyautatawa ga dan adam muuslmi da wanda ba musulmi ba.
Bayanin ya ce da dama daga cikin mabiya addinin muslunci a cikin kasashen turai sun fito ne daga kasashen larabawa da kuma Turkiya gami da kasashen nahiyar Afirka, karbar addinin muslunci da ake yi a cikin wadannan kasashe ya sanya gwamnatoci musamman ma irin su Faransa daukar matakan dakile yaduwar addini a cikin kasarta da ma sauran kasashen naiyar wadda mafi yawan mazaunata mabiya ddinin kirista ne.
1256041