IQNA

Ayatullahi Kashani Ya Bukaci Al'umma Masar Da 'Yantar Da Kansu Daga Makircin Makiya

20:14 - July 13, 2013
Lambar Labari: 2560721
Bangaren siyasa, Limamin da ya jagoranci sallar juma'a a birnin Tehran na kasar Iran ya jaddada cewar ta hanyar zurfafa tunani da hangen nesa ne kawai al'ummar Masar zasu kai ga 'yantar da kansu daga makircin makiya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, A hudubar sallar juma'ar a birnin Tehran a yau Ayatullahi Muhammad Imami Kashani ya tabo dambaruwar siyasar da ke faruwa a kasar Masar, inda ya jaddada cewar matukar al'ummar Masar suka zurfafa tunani da hangen nesa zasu kai ga rusa makircin da ake kitsawa kansu da nufin ganin kasarsu ta wargaje.
Ayatullahi Imami Kashani ya fayyace cewar kasar Masar kasa ce mai dadadden tarihi musamman a fannin al'adu, bincike, ilimin Musulunci, harkar noma da sana'o'in hannu, kuma al'ummar kasar sun bude ido ne a Musulunci don haka makiya suke kokarin ganin sun wurga su cikin rikici. Sakamakon haka Ayatullahi Imami Kashani ya yi kira ga al'ummar Masar da su dauki matakin hada kai domin warware sabanin da ke tsakaninsu ta hanyar gudanar da zaman tattaunawa da sulhu.
Dubban magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi a daga sassa daban-daban na kasar Masar, sun gudanar da wani gangami a jiya a wani makeken fili da ke gaban masallacin Rabi'at Adwiyya a cikin birnin Alkahira, domin kira da adawo da hambararren shugaban kasar Muhammad Morsi kan karagar shugabancin kasar.
Masu gangamin dai suna dauke da kwafi-kwafi na alkur'ani mai tsarki a hannunuwansu na dama da kuma totocin kasar Masar a hannuwansu an hagu, inda suke rera taken halascin shugabancin kasar Masar yana ga Muhammad Morsi ne kawai, yayin da daya daga cikin jagororin kungiyar 'yan uwa musulmi Safwat Hijazi ya gabatar da jawabi mai tsawo a gaban dubban magoya bayan kungiyar, inda ya ce za su ci gaba da kasancewa a wurin ko da za su kai wata daya ko watanni biyu, har ma sheka ko shekaru biyu, har sai an dawo da Muhammad Morsi a kan shugabancin kasar Masar.
1255979

captcha