Bangaren kasa da kasa, magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi a daga sassa daban-daban na kasar Masar, sun gudanar da wani gangami a jiya a wani makeken fili da ke gaban masallacin Rabi'at Adwiyya a cikin birnin Alkahira, domin kira da adawo da hambararren shugaban kasar Muhammad Morsi kan karagar shugabancin kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Masu gangamin dai suna dauke da kwafi-kwafi na alkur'ani mai tsarki a hannunuwansu na dama da kuma totocin kasar Masar a hannuwansu an hagu, inda suke rera taken halascin shugabancin kasar Masar yana ga Muhammad Morsi ne kawai, yayin da daya daga cikin jagororin kungiyar 'yan uwa musulmi Safwat Hijazi ya gabatar da jawabi mai tsawo a gaban dubban magoya bayan kungiyar, inda ya ce za su ci gaba da kasancewa a wurin ko da za su kai wata daya ko watanni biyu, har ma sheka ko shekaru biyu, har sai an dawo da Muhammad Morsi a kan shugabancin kasar Masar.
A cikin 'yan kawanakin da suka gabata ne jagoran kungiyar Muhammad Badi ya gabatar da jawabi a gaban magoya bayan kungiyar da suke zaman dirshan a masallacin Rabi'at Adwiyyah, inda ya shelanta cewa za su sadaukantar da kansu ta hanyar yin shahada a tafarkin dawo da Muhammad Morsi kan shugabancin kasar Masar, kwana guda bayan wannan jawabin ne wasu daruruwan magoya bayan kungiyar ta 'yan uwa musulmi suka kai samame kan wani babban gini na ma'aikatar tsaro da ake zaton cewa a wurin ne ake tsare da Muhammad Morsi, inda suka yi ba-ta-kashi tsakaninsu da sojojin da ke gadin wurin, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar magoya bayan kungiyar fiye da 40, da kuma wani babban jami'in soji guda tare da jikkatar wasu.
A nasa bangaren Firayi ministan rikon kwaryar kasar ta Masar Hazim Bilawi ya fadi a jiya Juma'a cewa, yana ci gaba da tattaunawa da bangarorin siyasar kasar domin kafa gwamnati, inda ya ce yana sa ran fara tattaunawa da mutanen da za su rike mukaman ministoci a ranar Lahadi ko Litinin mai zuwa, ya ce babu abin da zai hana kungiyar 'yan uwa musulmi shiga cikin gwamnatin rikon kwaryar da za a kafa, amma tuni kungiyar ta yi watsi da wannan batu.
1258468