IQNA

An nuna hotunan sheikh Hassan Shuhata a baje kolin sha'abaniyyah

23:16 - July 15, 2013
Lambar Labari: 2561998
Bangaren kasa da kasa, an nuna hutnan babban malamin addinin muslunci kuma jagoran mabiya mazhabar iyalan gidan amnzon allaha kasar Masar sheikh Hassan shehata da mabiya tafarkin takfiriyyah suka yi wa kisan gilla tare da tunzurawa daga Muhammad Morsi.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya an nuna hutnan babban malamin addinin muslunci kuma jagoran mabiya mazhabar iyalan gidan amnzon allaha kasar Masar sheikh Hassan shehata da mabiya tafarkin takfiriyyah suka yi wa kisan gilla tare da tunzurawa daga Muhammad Morsi da sojoji suka hambarar da shi daga shugabancin kasar.

A wani labarin kuma a karon farko tun bayan hambarar da tsohon shugaban kasar Masar Muhammad, ministan tsaron kasar Janar Abdulfattah Sisi ya gabatar da jawabi dangane da dalilain da suka sanya rundunar sojin kasar daukar wannan mataki kan hambararren shugaban.

A lokacin da yake gabatar da jawabin nasa a gaban manyan hafsoshin soji da kuma manyan jami'an tsaro na kasar Masar a jiya, ministan tsaron kasar Janar Sisi ya bayyana cewa, halascin kowane irin mulki da shugabanci yana hannun al'umma ne, a lokacin da akasarin al'ummar kasar Masar suna nuna rashin gamsuwarsu da mulkin morsi, sojoji sun nemi da a gudanar da kuri'ar raba gardama kan makomar shugabancinsa, domin kada kasar ta fada cikin mummunan yanayi na rikici, amma Morsi ya yi watsi da wannan kira.

Ya ce a kan haka rundunar sojin kasar ta dauki wannan mataki domin karba kiran jama'ar kasar, domin tabbatar da cewa an kare wa jama'a juyin juya halin da suka yi wanda a cewarsa Morsi ya kama wani salon mulki wanda ya yi hannun riga da juyin da al'ummar Masar suka yi, ya ce sojoji ba za su taba shiga cikin harkokin mulki da siyasar kasar ba, kuma kofa bude take ga dukkanin bangarorin siyasar kasar su shiga a dama da su a cikin harkokin siyasa da mulkin kasar bisa zabin jama'a.

1257861




captcha