Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa wasu rahotanni sun ce an killace gidan malamin gwamnatin qatar kuma daya daga cikin malamn kungiyar yan uwa musulmi mai tsananin kiyayya da mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah yusuf qardawia birnin alkahira na kasar Masar, bayan tabbatar da cewa shi ne yake tunzura 'yan ta'adda masu aki hari kan jami'an tsaro.
Ministan tsaron kasar Janar Abdulfattah Sisi ya gabatar da jawabi dangane da dalilain da suka sanya rundunar sojin kasar daukar wannan mataki kan hambararren shugaban. A lokacin da yake gabatar da jawabin nasa a gaban manyan hafsoshin soji da kuma manyan jami'an tsaro na kasar Masar a jiya, ministan tsaron kasar Janar Sisi ya bayyana cewa, halascin kowane irin mulki da shugabanci yana hannun al'umma ne, a lokacin da akasarin al'ummar kasar Masar suna nuna rashin gamsuwarsu da mulkin morsi, sojoji sun nemi da a gudanar da kuri'ar raba gardama kan makomar shugabancinsa, domin kada kasar ta fada cikin mummunan yanayi na rikici, amma Morsi ya yi watsi da wannan kira.
Ya ce a kan haka rundunar sojin kasar ta dauki wannan mataki domin karba kiran jama'ar kasar, domin tabbatar da cewa an kare wa jama'a juyin juya halin da suka yi wanda a cewarsa Morsi ya kama wani salon mulki wanda ya yi hannun riga da juyin da al'ummar Masar suka yi, ya ce sojoji ba za su taba shiga cikin harkokin mulki da siyasar kasar ba, kuma kofa bude take ga dukkanin bangarorin siyasar kasar su shiga a dama da su a cikin harkokin siyasa da mulkin kasar bisa zabin jama'a a kasar.
1258149