Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga wasu kafofin yada labarai na kasar Masar cewa wasu daga cikin magoya bayan hambararren shugaban kasar Masar Muhammad Morsi sun killace babban ginin jami'ar Azhar da ke birnin Alkahira bayan kin amincewa da ci gaban shugabancinsa wanda al'ummar kasar suka nuna rashin amincewa da shi kafin hambarar da shi a makon da ya gabata.
A wani rahoton kuma an kai hari akan sojojin Masar da su ke a yankin Saharar Sina da ke kasar Masar, kamfanin Dillancin Labarun Reuters ya nakalto cewa; maharani sun harba makamai masu linzami akan wani sansanin sojan Masar a yankin Sina da ke da iyaka da yankin Gaza na Palasdinu.
Kawo ya zuwa yanzu babu cikakken bayani akan girman asarar da harin ya haddasa, tun bayan kifar da gwamnatin Muhammadu Mursi na kungiyar ‘yan’uwa musulmi, masu dauke da makamai a yankin na Sina su ka tsananta kai hare-hare akan jami’an.
1258715