Bangaren kasa da kasa, magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi a kasar Masar Magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi a kasar Masar suna gudanar da wata zanga-zanga da suka fara a yammacin yau a wasu daga cikin manyan biranan kasar, da nufin matsa lamba kan sabbin mahukuntan kasar da su sarki Morsi kuma su mayar da shi kan kujerar shugabancin kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, rahotanni sun ce wasu daga cikin masu zanga-zangar sun nufi babban ginin majalisar ministocin kasar, inda suka nemi kutsa kai a cikin harabar ginin, amma jami'an tsaro sun hana su, wannan mataki dai ya zo kwana daya rak bayan rantsar da sabbin ministocin gwamnatin rikon kwaryar kasar da aka kafa bayan kifar da Morsi, wadda kungiyar 'yan uwa musulmi ke kallonta matsayin gwamnatin da ba halastacciya ba.
A jiya ne wasu masu dauke da makamai suka kai farmaki kan wasu jami'an soji a tsibirin Sina, inda suka jikkata wasu daga cikinsu, daya daga cikin jagororin kungiyar yan uwa muslmi Isam Iryan ya bayyana cewa, idan sabbin mahukuntan kasar suna son ganin an kawo karshen hare-hare kan sojojin kasar, to su gaggauta sakin Morsi tare da mayar da shi kan kujerar shugabancin kasar Masar.
Masu goyon bayan kungiyar 'yan uwa musulmi a kasar Masar Magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi a kasar Masar
suna gudanar da wata zanga-zanga da suka fara a yammacin yau a wasu daga cikin manyan biranan kasar, da nufin matsa lamba kan sabbin mahukuntan kasar da su sarki Morsi kuma su mayar da shi kan kujerar shugabanc.
1259440