Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, yanzu haka dai ana ci gaba da yin Allawadai da matakin da kungiyar tarayyar turai ta dauka na saka kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda na duniya tare da matsin lambar Amurka.
A nasa bangaren Shugaban kasar Lebanon M. Sulaiman ya kirayi kungiyar tarayyar turai da ta sake yin nazari kan matakin da ta dauka, na saka abin da ta kira bangaren soji na kungiyar Hizbullah a cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda.
Sulaiman ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da wakiliyar kungiyar tarayyar turai a kasar Lebanon Angelina Jhorest, inda ya bukaci karin haske daga gare ta kan wannan mataki mai hadari da kungiyar ta dauka a kan Hizbullah.
Ya ce day a kamata kungiyar tarayyar turai ta yi tunani kafin daukar wannan mataki, kum ayanzu ma yana kiranta da ta sake yin nazari kan hakan, domin babu maslaha ta siyasa a cikin hakan, domin kuwa a cewarsa ya kamata kungiyar tarayyar turai ta yi abin da zai kara tabbatar da zaman lafiya ne a Leanon tare da karfafa alaka ta siyasa, maimakon akasin hakan.
1262336