IQNA

Kungiyar Hizbullah Ta Ce Kudirin Tarayyar Turai A Kanta Ba Shi Da Kima

17:46 - July 23, 2013
Lambar Labari: 2566005
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar da wani bayani da a cikinsa ta bayyana cewa, kudirin tarayyar turai da ya saka ta a cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda hakan ba shi da wata kima, domin kuwa kudiri ne da haramtacciyar kasar Isra'ila ta shirya ta mika wa tarayyar turai, ita kuma ta amince da shi bisa matsin lambar Amurka.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, bayanin ya ce babu wani abu wai shi bangaren soji na kungiyar Hizbullah, domin kuwa kungiya daya ce mai yaki da zaluncin haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummar musulmi, tare da kore duk wata farfaganda da ke cewa kungiyar ta mallaki kamfanoni ko wuraren kasasuwanci ko kudade ko makamai a wasu kasashen ketare, inda bayanin ya ce duk wannan na daga cikin makircin da ake kitsa wa kungiyar, ta hanyar haratacciyar kasar Isra'ila gami da Amurka da kuma hadin baki da wasu gwamnatoci.

Jim kadan bayan amincewa da wannan kudiri da ministocin harkokin wajen kasashen tarayyar turai suka yi a birnin Brussel na kasar Belgium, gwamnatocin Amurka da Isra'ial suka fito suka yi na'am tare da nuna matukar farin cikinsu da hakan.

Kungiyar Hizbulla..ta maida martani kan matakin da kungiyar Tarayyar Turai ta dauka na sanya Kungiyar a jerin kungiyoyi ‘yan ta’adda na Dunia. Gidan talvijin na Almayadin ya habarta cewa kungiyar Hizbull…tace matakin da Tarayyar turai ta dauka ba ta yiwa kungiyar adalci ba.kungiyar Turai ta mika wuya ga kasar Amurka ,daukan wannan mataki ba zai sa su samu guri a kasashen larabawa da na Musulmi ba. Matakin da Tarayyar Turai ta dauka na sanya kungiyar ta huzbull…shi ke nuna tarayyar turai ta mika wuya kan matsin lamba da haramcecciyar kasar Isla’ila ke yi mata.
Gidan talvijin na Almanar yayin da yake zarkin kasar Birtaniya wajen yin zagon kasa na yaki da kungiyar hizbull…ya bayyana cewa HKI tayi amfani da tarayyar Turai wajen sanya kungiyar hizbull…a jerin kungiyar ‘yan ta’adda .HKI a tsahon shekaru tayi ta kokari ba tare da kakkautawa ba tare da koyan bayan kasashen Birniya da Amurka na ganin ta tilastawa kungiyar tarayyar Turai daukan wannan Mataki.

1262398

captcha