IQNA

Sabani Tsanain Malamin jami'ar Azhar Da Yusuf Qardawi

18:03 - July 27, 2013
Lambar Labari: 2567640
Bangaren kasa da kasa, a daidai lokacin da malamin gwamnatin Qatar kuma daya daga cikin muggan malamai da suke fitar da fatawar kisan musulmi a duniya Yusuf Qardawi yake haramta fita domin goyon bayan sojojin Masar, babban malamin jami'ar Azhar ya yi kira da afita domin goyon bayan sojoji.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin da malamin gwamnatin Qatar kuma daya daga cikin muggan malamai da suke fitar da fatawar kisan musulmi a duniya Yusuf Qardawi yake haramta fita domin goyon bayan sojojin Masar, babban malamin jami'ar Azhar ya yi kira da afita domin goyon bayan sojoji a suka hambarar da Muhammad Morsi.

A wani labarin kuma Ministan cikin gidan Masar ya bayyana cewa nan zuwa wasu kwanuka za su kawo karshen taruwar ‘yan adawa a babban birnin Kasar. Kanfanin reuteus ya habarta cewa Muhamad Ibrahim Ministan cikin gidan Masar a jiya juma’a ya bayyana cewa Gwamnati za tayi amfani da hanyoyin doka don tarwaza masu goyon bayan hanbarerren shugaban kasa Muhamad Mursi daga dandalin rabi’atul adawiya.

Ministan ya kara da cewa Ma’aikatarsa ta samu kararraki da dama daga mazauna birnin Alkahira kan taruwar ‘yan kungiyar ‘yan uwa musulmi a wannan guri.don haka ma’aikartar za ta dauki matakin da ya dace don tabbatar da tsaro a babban birnin Tun ranar 23 na watan yuni da ya gabata magoya bayan hanbarerren shugaban kasar suka taru a Dandalin Rabi’atul adawiya inda suka ce ba zasu bar gurin ba har sai an maido Muhamad Mursi kan karagar Milki.

Wasu majiyoyi a Masar sun ce fiye da mutane 120 ne suka rasa rayukansu sakamakon taho-mu-gama da aka yi tsakanin masu adawa da hambararren shugaban kasar Mohammad Morsi, da kuma 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi da ke neman a dawo da shi kan karagar shugabancin kasar.

A sanarwar da ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Masar ta bayar ta bayyana cewa mutane 20 ne suka rasa rayukansu sakamakon arangamar da bangarorin biyu suka yi, sai wasu majiyoyin sun ce adadin yah aura haka, yayin da majiyoyin kungiyar 'yan uwa musulmi ta Muhammad Morsi ta ce adadin ya haura mutane 120, kuma akasarinsu 'ya'yan kungiyar ne.

Miliyoyin mutane ne dai suke ci gaba da gudanar da zanga-zanga a Masar tun daga jiya Juma'a, inda masu goyon bayan Morsi suka taru a masallacin Rabi'at Adwiyyah a birnin Alkahira, masu adawa da shi kuma suka cikin dandalin Tahrir, da Ittihadiyya, kamar yadda aka gudanar da irin wannan gangami na bangarorin biyu a biranan kasar.


1263902




captcha