IQNA

Malaman addini duk suna kira domin raya ranar Qods

17:59 - August 01, 2013
Lambar Labari: 2569635
Bangaren kasa da kasa, manyan malman addinin muslunci a kasar Iran da ma wasu daga cikin kasashen musulmi suna ci gab ada yin kira da raya ranar Qods domin tunatar da duniya halin da masallaci mai alfarma yake ciki karkashin mamayar yahudawan sahyuniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga wasu shafukan yanar gizo cewa manyan malman addinin muslunci a kasar Iran da ma wasu daga cikin kasashen musulmi suna ci gab ada yin kira da raya ranar Qods domin tunatar da duniya halin da masallaci mai alfarma yake ciki karkashin mamayar yahudawan sahyuniya 'yan kaka gida.

Jaridar Daily Telegraph ta kasar Birtaniya ta bayar da wani rahoto a bugunta nay au Alhamis cewa, tsohon jakadan kasar Afirka ta kudu a haramtacciyar kasar Isra'ila Ismail Coovadia ya bayyana gwamnatin yahudawan da cewa gwamnatin wariya ce a kan palastinawa.

Jaridar ta ce furucin na tsohon jakadan kasar Afirka ta Kudu a haramtacciyar kasar Isra'ila ya fusata mahukuntan Tel Aviv matuka, inda ta nakalto daga gare shi yana cewa, "sun ba ni kyauta a lokacin da nake shirin tafiya bayan kammala aikina a shekara ta 2012, amma naki karbar wannan kyauta da Isra'ila ta yi mani.

Coovadia ya ce sun nemi suka dasa wasu ita ce da sunana, na ce ban amince da hakan ba, domin kuwa na san kasar da za a dasa wadannan ita ce da sunana, kasa ta sata daga cikin kasar Palastinawa, kuma ni mutum ne da yi yi gwagwarmaya da mulkin wariya a Afirka ta kudu, kuma abin da na gani a Isra'ila iri daya da mulkin wariyar da aka yi mana a kasarsu.

1266735




captcha